Kuru Fasulye, ɗaya daga cikin shahararrun abincin gargajiya da aka fi so a Turkiyya, alama ce ta al’adar ƙasar, wanda Turkawa ke matuƙar so saboda ya samo asali ɗaruruwan shekaru da suka wuce.
Halima Umar Saleh ta TRT Afrika ta ce yana daga cikin abincin Turkawa da ta fi so sosai, don haka ta ja mu cikin kicin ɗinta yayin da take girka wannan daddaɗan abinci, tare da gabatar da shi kamar yadda aka saba yi a kasar, wato da dafaffiyar farar shinkafa mai laushi da kuma pickles masu ɗan tsami a cikin salad.
Domin samun ƙarin bayani game da abincin Turkiyya da ɗimbin al’adunsu da girke-girken da suka yi gado, ku ziyarci:
