Hatsarin ya faru ne a yankin Mile 3 da ke Gombe a ranar Laraba, yayin da tirelar ke tafiya a kan titin Gombe zuwa Yola.
Shaidun gani da ido sun bayyana cewa direban motar ya yi ƙoƙarin kauce wa haddasa mummunan bala’i ta hanyar karkatar da motar daga hanyar da take bi. Sai dai kuma tirelar ta kutsa cikin wasu motoci, shagunan bakin hanya da kuma mutanen da ke kusa da wurin.
Rahotanni sun nuna cewa mutum bakwai ne tirelar ta buge a lokacin hatsarin, inda aka ce mutum uku sun mutu nan take, yayin da sauran suka samu raunuka daban-daban.
