An sake samun rahoton barkewar cutar Ebola a DR Congo, yayin da kasashen Afirka ke fara daukar matakan kariya.
Amma mece ce Ebola? Ta yaya take yaduwa? Kuma ta yaya za ku kare kanku da iyalanku?
Ku kalli wannan bidiyon domin sanin gaskiya game da daya daga cikin cututtuka mafi hatsari a duniya.
