| Hausa
Kasashe 50 sun shiga atisayen sojin Turkiyya na Fees - 2026
00:45
Kasashe 50 sun shiga atisayen sojin Turkiyya na Fees - 2026
Ƙawayen ƙungiyar NATO kamar Amurka da Faransa da Birtaniya sun gudanar da atisayen tare da sauran ƙasashe abokan hulɗa na duniya, ciki har da Azerbaijan da Pakistan da Japan da Rwanda.

Ƙasashe 50 ne suka hallara a Izmir domin halartar atisayen haɗin gwiwar harbe-harbe kai-tsaye na Efes-2026 da Turkiyya ta shirya. Atisayen na wannan shekara ya mayar da hankali kan gungun jiragen yaƙi marasa matuƙa masu sarrafa kansu, jiragen yaƙi marasa matuƙa da ake harbowa daga jiragen ruwa masu ɗaukar jirage, da kuma tsarin kariyar sararin samaniya mai matakai daban-daban da ƙasar ta ƙera da kanta.

Ƙawayen ƙungiyar NATO kamar Amurka da Faransa da Birtaniya sun gudanar da atisayen tare da sauran ƙasashe abokan hulɗa na duniya, ciki har da Azerbaijan da Pakistan da Japan da Rwanda.

Abin lura shi ne, atisayen ya kasance karo na farko da sojojin Siriya suka halarta, sannan kuma ya samu nasarar haɗa sojoji masu gaba da juna daga yammaci da gabashin Libya.

Ƙarin Bidiyoyi
Alhazai sun hau Dutsen Arfa
Yadda aka ayyana Pantami a dantakarar gwamnan Gombe a PDP
Ethnosport: Ana bikin wasannin gargajiya na duniya a Istanbul
Yadda wata babbar mota ta kwace ta yi ajalin mutum hudu a Gombe
'Yansandan New York sun kama mutumin da ya yi wa Musulmai barazana da wuka
Sharhi kan nasarar cin kofin Premier da Arsenal ta yi
Wadanda suka yi harbe-harbe sun dauki bidiyon harin kai-tsaye
Guguwa ta mayar da sararin samaniyar Najaf a Iraqi ruwan goro
Mece ce cutar Ebola? Ta yayya za a kare kai da kuma shawo kan cutar?
Mun zo Turkiyya don tattauna kan yadda za mu inganta haddace Alkur'ani