Bikin na shekara-shekara da ake yi washegarin Sallar Layya, na wakiltar al’adu, haɗin kai da zumunci, inda ake raye-raye da kaɗe-kaɗe, yayin da mahalarta daga rukunin shekaru da matsayi daban-daban ke shiga shagulgulan cikin kayatattun tufafin gargajiya.
Ana kallon bikin Ojude Oba a matsayin ɗaya daga cikin manyan bukukuwan al’adu mafi muhimmanci a yankin, inda yake jan hankalin baƙi daga cikin Nijeriya da ma ƙasashen waje
