| Hausa
An kashe mutum daya, an jikkata 63 ahare-haren Iran a filin jirgin saman Kuwait
00:32
An kashe mutum daya, an jikkata 63 ahare-haren Iran a filin jirgin saman Kuwait
Ma'aikatar Lafiya ta Kuwait ta ce mutum guda ya rasa ransa, yayin da aƙalla mutane 63 suka jikkata, ciki har da ma'aikatan filin jirgin sama da fasinjoji.

Bidiyon da shaidu suka ɗauka sun nuna mummunar ɓarna da aka samu a Filin Jirgin Sama na Ƙasa da Ƙasa na Kuwait a ranar Laraba, inda aka ga gobara na ci sannan hayaƙi ya mamaye sararin samaniya bayan hare-haren jirage marasa matuƙa da makamai masu linzami. Sai dai Iran ta musanta hannu a harin.

Ma'aikatar Lafiya ta Kuwait ta ce mutum guda ya rasa ransa, yayin da aƙalla mutane 63 suka jikkata, ciki har da ma'aikatan filin jirgin sama da fasinjoji.

Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta ƙasar ta bayyana cewa kamfanin jirgin saman Kuwait Airways ya ci gaba da gudanar da zirga-zirgarsa daga Terminal 4 bayan tantance irin ɓarnar da aka yi da kuma ɗaukar matakan tsaro.

Dakarun kare juyin-juya-halin Musulunci na Iran sun musanta cewa sun kai hari kan Filin Jirgin Sama na Kuwait, suna masu cewa ɓarnar da aka samu a wani sashe na tashar fasinjoji ta samo asali ne sakamakon matsalar aiki da makamin kariya daga hare-haren sama na Patriot da Amurka ta ƙera.

A wata sanarwa, Ma'aikatar Harkokin Wajen Iran ta ce hare-haren da aka kai kan Kuwait da Bahrain matakin kare kai ne bayan Amurka ta kai hari kan wani jirgin dakon mai na Iran a Mashigar Hormuz da kuma wata hasumiyar sadarwa a Tsibirin Qeshm.

Ma'aikatar ta kuma ce ƙasashen Kuwait da Bahrain suna da "alhaki kai tsaye kuma a sarari" kan hare-haren, tana zargin cewa an yi amfani da ƙasashensu da wasu cibiyoyinsu wajen tallafa wa hare-haren da Amurka ta kai kan Iran.

Ƙarin Bidiyoyi
Shugaba Erdogan ya karbi bakuncin Tiani na Nijar a birnin Ankara na Turkiyya
Jam'iyyun siyasa da 'yantakararsu a zaben shugaban kasa na 2027
Gobarar New Delhi ta halaka mutum 21
Ojude Oba: Bikin al'adar gargajiya da ake gudanarwa bayan babbar Sallah
Jiragen ruwan Iran masu gudun tsiya na tsintiri a mashigar Hormuz, in ji gidan talabjin din gwamnati
''Dole mu kashe tunanin za a iya samar da kasar Falasdinawa''
Sabon shugaban kasar Benin ya kai ziyara Nijar
Iran ta sanar da 'harin ramuwar gayya' a tekun Oman
Isra'ila ta kai hare-hare da dama a kusa da asibitin Jabal Amel a Lebanon
Batun satar dalibai da malamai a jihar Oyon Nijeriya