| Hausa
An kyankyashe dubban tsuntsayen flamingo a Turkiyya
01:17
An kyankyashe dubban tsuntsayen flamingo a Turkiyya
An ƙyanƙyashe dubban jariran tsuntsayen flamingo a Tafkin Tuz, wanda ke zama ɗaya daga muhimman wurare masu dausayi na ƙasar Turkiyya, kuma ɗaya daga cikin manyan wuraren rayuwar flamingo na duniya.

Tafkin, wanda ke kan iyakokin lardunan Ankara, da Konya, da Aksaray, yana zama mazaunin tsuntsayen flamingo sabbin jini, bayan kammala ƙyanƙyasar ƙwayayensu.

An ga ƙananan tsuntsayen suna girma a ƙarƙashin kulawar iyayensu, yayin da suke koyon dabarun rayuwa masu mahimmanci, da suka haɗa da neman abinci, da zirga-zirga a faɗin tafkin, da kuma kauce wa haɗurran da za su iya fuskanta a wuraren da suke rayuwa.

Karuwar yawan ruwa da kuma zuwan dubban jariran tsuntsayen sun janyo hankalin masu sha'awar yanayi da masu ɗaukar hoto na namun daji zuwa tafkin, wanda ke ci gaba da kasancewa ɗaya daga mafi muhimmancin tsarin muhalli na yankin.

Ƙarin Bidiyoyi
Abubuwan da Dala Triliyan 1.1 ta Elon Musk za ta iya yi a Afirka
Jirgi mara matuki na Isra'ila ya kai wa danjaridar Lebanon hari
Manyan sojojin da rashin tsaro ya yi ajalinsu a Nijeriya
Yadda aka sauya rigar ka'aba a ranar farko ta shekarar musulunci
An jera dubban takalma a don girmama 'ya'yan Falasdinawa da aka kashe
Yadda waya da soshiyal midiya ke lalata kwakwalwar yara
'Dalilin da ke sa ake sauya jarumai a fina-finai masu dogon zango'
Masu adawa da tsarin mulkin masarauta sun gudanar da tattaki yayin faretin bikin Sarki Charles
'Yasandan Peru sun yi shigar burtu dom kama masu laifi
Gobara ta cinye rukunin ma'ajiyar kayan aikin likitanci a California