Wani bincike da Ma’aikatar Sadarwa, Kirkire-kirkire da Tattalin Arziki na Zamani ta Nijeria ta gudanar a baya-bayan nan ya bayyana cewa fiye da ’yan Nijeriya kaso 80 cikin 100 da aka tattauna da su, sun goyon bayan kafa wasu dokoki na takaita amfani da kafofin sadarwa na zamani ga yara ’yankasa da shekara 16.
Masana dabi’un dan’adam da likitocin kwakwalwa na wannan zamani suna yawan gargadi kan yawan amfani da soshiyal midiya da wayar salula, inda suke cewa suna haddasa ‘Gagarumin Sauyi a Tsarin Kwakwalwar Yara’ wato abin da suka yi wa lakabi da (The Great Rewiring) a Turancin Ingilishi.
