Da yake magana da manema labarai game da yiwuwar tashin hankali tsakanin Turkiyya da Isra’ila, Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi watsi da irin wannan damuwa, yana mai cewa zai shiga tsakani da kansa idan bukatar hakan ta taso.
Trump ya yaba wa Shugaban Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan, inda ya bayyana shi a matsayin “babban jagora” kuma aboki na kusa.
