Daga Gaza zuwa Lebanon da kuma batun Iran, Shugaban Amurka Donald Trump ya sha jan kunnen Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu, har ma a wani lokaci ana zargin ya kira shi "mahaukaci". Amma duk da matsin lamba, Netanyahu ya ci gaba da tafiyar da manufofinsa.
Shin Trump ya gaza rinjayar Netanyahu ne? Ko kuwa Firaministan Isra’ilan na amfani da yaƙi a matsayin makamin tsira a siyasa? Ku kalli sharhi kan yadda manyan saɓani biyar tsakanin shugabannin biyu suka wakana da abin da ya biyo baya.
