Wata ɗalibar makaranta daga Ingushetiya (jamhuriya mai yawan Musulmi a Rasha), Fatima Mammatova ta fuskanci kalamai masu tada ƙura a wata gasar ilimin tarihin jiragen sama ta ƙasa da ƙasa, bayan da wata mambar alkalai daga Sabiya, Radmila Tonkovic ta tambayi dacewar saka hijab ɗinta.
Tattaunawar ta karkata daga binciken da ta gudanar zuwa yanayin shiagarta, lamarin da ya jawo suka a kafafen sada zumunta.
Rahotanni sun ce har yanzu ba wanda ya bayar da hakuri daga mambar tawagar alkalan ko masu shirya gasar.
