| Hausa
Turkiyya ta kai wa fararen-hula a Lebanon kayan abinci sakamakon hare-haren Isra'ila
01:10
Turkiyya ta kai wa fararen-hula a Lebanon kayan abinci sakamakon hare-haren Isra'ila
Turkiyya ta kai tan 360 na kayan agaji ga fararen-hula a Lebanon waɗanda hare-haren Isra’ila suka raba da muhallansu.

Kayan agajin sun haɗa da barguna, katifu, jakunkunan bacci, tantuna, kayan abinci da kuma kayayyakin agajin gaggawa. Jami’ai sun ce za a ci gaba da kai irin wannan taimako yayin da fiye da mutane miliyan 1 da suka rasa matsugunansu a Lebanon ke fuskantar mawuyacin hali na jinƙai.

Tun bayan da Isra’ila ta fara kai hare-hare a 2024, Turkiyya ta riga ta kai sama da tan 1,700 na kayan agajin jin ƙai zuwa Lebanon.

Ƙarin Bidiyoyi
Mutanen da ake dauka haya don su yi kuka lokacin jana'iza
Takaddama kan saka hijabi a gasar Olympiad a Rasha
Gagarumar guguwa mai dake da kura ta mamaye yankin Xinjiang na China
IPU: Abin da ya faru a taron kungiyar 'yanmajalisu ta duniya a Istanbul
Gargadin NBC ga kafofin yada labarai a Nijeriya
Taron Antaliya: Bajekolin kayan Afirka a babban taron diflomasiya na duniya
'Saura kadan kada ya cinye ni a wajen daukar fim a Kogin Kaduna'
Butum-butumi ya kafa bajintar duniya a gasar tsere ta Beijing
Taron Antaliya: Hada kai don zaman lafiya a yankin Falasdinu
WhatApp ya shiga tsaka mai wuya kan tsare-sirri