Mariam Al Astrulabi: wata mace mai ilimin taurari
AlʿIjliyyah bint al-ʿIjliyy, wadda aka fi saninta da suna Mariam al Astrulabi a ƙasashen Yammacin duniya, 'yar ƙasar da a yanzu ake kira Siriya, masaniyar kimiyya ce a ƙarni na 10 wadda ta yi fice a fannin ilimin taurari.
Ta ƙirƙiro na'urar astrolabe wadda ke kiyaye lokaci da gane matsayar taurari domin yi wa mutane jagora a tafiye-tafiye a faɗin duniya.
Aikinta ya samu karɓuwa sosai inda ta taimaka wajen fayyace lokutan sallah da nuna alƙibla da ɗaukar azumin Ramadan.