Tsohon shugaban hukumar leƙen asirin Isra’ila ta Mossad, Tamir Pardo, yayin wata ziyara domin bibiyar tashin hankalin da wasu Yahudawa ‘yankama-wuri-zauna ke yi ba bisa ƙa’ida ba a Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye, ya kwatanta abubuwan da ya gani da Holocaust.
Pardo ya taba zama babban janar a rundunar sojin Isra’ila, kuma ya rike mukamin daraktan Mossad daga shekarar 2011 zuwa 2016.
