Ɗaya daga cikin malaman da aka sace tare da ɗalibai yayin harin da 'yanbindiga suka kai wa al'ummar Ahoro-Esiele da ke Ƙaramar Hukumar Oriire a Jihar Oyo ranar 15 ga Mayu ta bayyana matuƙar godiya ga shugaban ƙasa Bola Tinubu da jami'an tsaron Nijeriya bayan an ceto tare da kuɓutar da dukan ɗalibai da malaman.
Da take bayani a madadin sauran waɗanda aka kuɓutar, malamar ta jaddada cewa ba don ƙoƙarin shugaban ƙasa ba da tuni an kashe su.
