Gwamnatin Philippines ta ce jami'an Rundunar Tsaron Gabar Tekun China sun bugi wani jami'in rundunar ruwanta a kai da sandar katako, tare da lalata wani ƙaramin jirgin ruwa na roba.
Sai dai China ta musanta zargin, tana mai cewa Philippines ce ta tayar da rikicin.
Rundunar Tsaron Gabar Tekun China ta kuma bayyana cewa za ta ci gaba da gudanar da ayyukan tabbatar da doka a yankin.
