Ya ce duniya na fuskantar babbar barazanar da ta shafi wanzuwar rayuwar ɗan'adam, sakamakon yawan amfani da albarkatun ƙasa fiye da ƙima, yana mai gargaɗin cewa babu wata ƙasa da illolin sauyin yanayi za su ƙyale.
Turkiyya ce ta karɓi baƙuncin taron shugabannin ƙasashe na COP31 a karon farko, inda shugabannin ƙasashe daban-daban suka hallara a Antalya domin tattaunawa kan matakan yaƙi da sauyin yanayi a duniya.
