Dr Islam Eldeh, wani likitan yara kuma ƙwararre kan kula da jariran da aka haifa, da ke birnin Alkahira na Masar ne ya wallafa bidiyon a ranar Lahadi, lamarin da ya sa mutane ke yin hasashe cikin raha kan abin da jaririn ke tunani.
Yayin da wasu ke ganin yanayin natsuwar jaririn abin sha’awa ne, wasu kuma na ganin kamar ya riga ya tsara dukkan abubuwan da zai yi a nan gaba, don haka babu abin da zai dame shi.