Za a iya cewa tsugunne ba ta kare ba ga wasu jam’iyyun siyasa a Nijeriya bayan Hukumar Zaɓen Ƙasar (INEC) ta ce jam’iyyun siyasa da suka tsayar da ’yantakarar da sunayensu ba sa cikin rijistar da suka miƙa wa hukumar ba za su samu damar tsayar da ’yan takarar ba a zaɓukan shekarar 2027.
Ko me hakan ke nufi ga wasu da ake tababa kan takararsu?
