| Hausa
Falasdinawa sun yi ban kwana da mutum 105 da suka mutu a hare-haren Isra'ila
Falasdinawa sun yi ban kwana da mutum 105 da suka mutu a hare-haren Isra'ila
Falasdinawa sun taru a Gaza domin gudanar da jana'izar mutane 105 da aka ciro gawawwakinsu daga ɓaraguzan wani gini a yankin Yarmouk; mutanen da aka kashe a hare-haren sama a farkon yaƙin kisan ƙare dangi da Isra'ila ta ƙaddamar a Gaza.

Daga cikin waɗanda suka rasa rayukansu akwai mata da yara, har da wata 'yarjaridar Falasdinu mai suna Doaa Sharaf da 'yarta.

An ajiye kyandir 105, da hotuna, da kayayyakin amfani tare da gawawwakin domin nuna girmamawa da jimami.

Ma'aikatar Lafiya ta Gaza ta bayyana cewa, saɓa yarjejeniyar tsagaita wuta ta watan Oktoban 2025 da Isra'ila ta yi, ta yi sanadiyyar mutuwar Falasdinawa 1,431 tare da jikkata wasu 5,026, yayin da adadin waɗanda suka mutu tun watan Oktoban 2023 ya haura 74,000.

Ƙarin Bidiyoyi
Rikicin Saudiyya da Houthi: Shin zai fadada a Gabas ta Tsakiya?
Kasashen Afirka da tattalin arzikinsu ya fi bunkasa
Rage farashin man fetur a Nijeriya na tsawon kwana 30
Akwai jam'iyyun da ba za su yi takarar wasu mukamai ba a zaben 2027 - INEC
Shirin INEC na fara amfani da AI a zaben Nijeriya na 2027
Sabanin da Ronaldo ya samu da kocin tawagar Portugal
Matsayin biredi a tsarin cin abinci da lafiyar dan'adam
Kalaman Shettima kan matsin tattalin arzikin da ake fama da shi a Nijeriya
Alwashin gwamnatin Nijar kan masu hannu cikin matsalar tsaron kasar
Sarkakiyar takarar PDP a Gombe: ko akwai sauran kalubale a gaban Pantami?