Shugaban Amurka Donald Trump ya yi watsi da martanin Iran ga shawarar Amurka ta baya bayan nan ta kawo ƙarshen yaƙi tsakanin ɓangarorin biyu.
“Yanzu na gama karanta martanin waɗanda ake ce wa ‘wakilan’ Iran. Ba na sonsa -- BA ZA A IYA LAMUNTA DA SHI BA KWATA-KWATA!” kamar yadda Trump ya bayyana a shafinsa na sada zumunta, Truth Social.
Saƙon ya zo ne sa’o’i bayan wata ƙafar watsa labaran gwamnatin ƙasar Iran ta ruwaito cewa Tehran ta tura martaninta ga Amurka ta hanyar masu shiga tsakani na Pakistan.
“Martanin Jamhuriyar Musulunci na Iran ga shawarar Amurka ta baya bayan nan ta kawo ƙarshen yaƙi an tura shi ga masu shiga tsakani na Pakistan a yau,” kamar yadda kamfanin dillancin labaran IRNA ya ruwaito.

Kafar watsa labarai ta ƙasar ta IRIB ta ce martanin ya mayar da hankali ne kan kawo ƙarshen yaƙin da Amurka da Isra’ila suka ƙaƙaba ta dukkan fannoni, musamman a Lebanon, da kuma tabbatar da tsaron jigilar kayayyaki ta ruwa.
Duk da tsagaita wuta tsakanin Isra’ila da Lebanon da ke wakana tun ranar 17 ga watan Afrilu, wanda daga baya aka tsawaita zuwa tsakiyar watan Mayu, rundunar sojin Isra’ila ta ci gaba da da kai hare-hare a ko wace rana a Lebanon da kuma musayar wuta da Hezbollah.
Tashin hankali a Gabas ta Tsakiya ya ƙaru tun lokacin da Amurka da Isra’ila suka ƙaddamar da hare-hare kan Iran ranar 28 ga watan Fabrairu, lamarin da ya haddasa ramuwar gayya daga Tehran kan Isra’ila da kuma ƙawayen Amurka a ƙasashen Larabawan da ke gaɓar teku, tare da rufe mashigar ruwan Hormuz.
An fara tsagaita wuta ranar 8 ga watan Afrilu ta hanyar shiga tsakani na Pakistan, amma tattaunawa a Islamabad ta gaza cim ma zaman lafiya mai ɗorewa.
Daga bayan shugaban Amurka Donald Trump ya tsawaita tsagaita wutar ba tare da wani wa’adi ba, lamarin da ya bai wa masu diflomasiyya damar neman mafita ta dindindin a yaƙin.
















