| Hausa
AFIRKA
2 minti karatu
Ghana ta kwashe 'yan ƙasarta 300 daga Afirka ta kudu yayin da ake zanga-zanga kan baƙin haure
Jirgin farko na 'yan Ghana da aka kwashe daga Afirka ta Kudu kan tashin hankalin da ake fuskanta dangane da baƙin haure ya sauka a Accra ranar Laraba.
Ghana ta kwashe 'yan ƙasarta 300 daga Afirka ta kudu yayin da ake zanga-zanga kan baƙin haure
Afirka ta Kudu ta fuskanci karuwar nuna kiyayya da cin zarafin baki a 'yan makonnin nan, sai dai gwamnati ta yi kira da a kwantar da hankula. / Reuters

Jirgin farko na 'yan Ghana da aka kwashe daga Afirka ta Kudu saboda tashin hankali kan baiƙn haure ya isa Accra a ranar Laraba, in ji Ma'aikatar Harkokin Wajen Ghana.

Ana sa ran cewa kimanin ‘yan Ghana 800 ne za su bar Afirka ta Kudu bayan Accra ta shirya jiragen maido da su saboda jerin zanga-zangar adawa da baƙi da ta ɓarke a ƙasar.

Wani mai ɗaukar hotuna na AFP ya ga ɗaruruwan 'yan Ghana suna tsaye a layi a Filin Jiragen Sama na O.R. Tambo, a wajen Johannesburg, da safiyar Laraba.

Matsayin rashin aikin yi

Shafin da ke bibiyar sufurin jiragen sama na FlightAware ya nuna cewa jirgin ya tashi bayan karfe 11:00 daidai na safe agogon Afirka ta Kudu.

Ofishin Jakadancin Ghana a Afirka ta Kudu ya ce ana sa ran mutane kusan 300 za su kasance a cikin jirgin farko, wanda aka tsara zai sauka ranar Laraba.

Gwamnatin Ghana ta yi alƙawarin bai wa waɗanda take mayarwa daga Afirka ta Kudu ƙunshin tallafin kuɗin sake shigar da su cikin al'umma da kula da lafiyar ƙwaƙwalwarsu da zamantakewa.

Afirka ta Kudu, wadda ta samu matakin rashin aikin yi fiye da 30%, ta sha fama da gangamin adawa da baƙin haure, ciki har da a 'yan makonnin baya bayan nan.

Gwamnatin Afirka ta Kudu ta yi kira ga 'yan ƙasarta da su yi haƙuri su kuma rungumi baƙin haure da suke cikin ƙasar bisa doka.