| Hausa
DUNIYA
2 minti karatu
Miliyoyin Musulmai sun taru a kan Dutsen Arfa yayin da aka kai ƙololuwar Aikin Hajji
Kimanin Musulmai miliyan 1.8 ne suka taru a Arfa don gudanar da ibada mafi girma a ayyukan Hajji.
Miliyoyin Musulmai sun taru a kan Dutsen Arfa yayin da aka kai ƙololuwar Aikin Hajji
Mahajjata musulmi suna yin addu'a a kan Dutsen Arafat, mafi mahimmancin rukunin aikin Hajji, yayin aikin hajjin shekara-shekara a Makka, kasar Saudiyya ranar 26 ga Mayu, 2026. / Anadolu Agency

Kimanin Musulmai miliyan 1.8 da ke gudanar da aikin hajji ne suka nufi filin Arfa a yammacin Saudiyya a ranar Talata don gudanar da ibada mafi girma a aikin hajji na shekara-shekara.

An tura jami'an tsaro da yawa kan hanyoyi da titunan don kula da taron jama'a tare da bin tsarin da aka amince da shi, in ji Kamfanin Dillancin Labarai na Saudiyya.

Kamfanin ya ruwaito cewa zirga-zirga a hanyoyi ta kasance cikin tsari, yayin da alhazai ke tafe daga Mina zuwa Arafat.

A Arafat alhazai sun yi ƙasarun sallar Azahar da La’asar a haɗe a Masallacin Namirah.

Bayan faɗuwar rana alhazan za su nufi Muzdalifah, inda za su yi sallar Magariba da Issha, sannan su kwana har zuwa washegari.

A ranar Litini aka fara ayyukan hajjin, yayin da alhazai suka isa Mina, a yammacin Saudiyya, cikin manyan tsaruka da matakan tsaro da aka tanada don saukaka aikin.

Lokacin Hajjin da za a yi a tsawon kwanaki shida sun haɗa da tsayuwar Arafat a ranar Talata, da kwana a Muzdalifah, da jifa da ɗawafin a Ka'aba masallacin harami na Makkah.

Ayyukan sun ƙunshi ibadu da dama waɗanda ke nuna muhimman ƙa'idojin addinin Musulunci, kuma suna tunawa jama’ar irin sadaukarwar da Annabi Ibrahim da iyalinsa. suka yi.

Hukumomin Saudiyya sun faɗaɗa matakan tsare-tsare da tsaro don kakar hajji ta 2026, ciki har da amfani da fasahar sa ido da tsarin kula da taron jama'a don tsara zirga-zirgar masu aikin hajjin da hana shiga wurare masu tsarki ba bisa ƙa’ida ba.