Wani rahoto daga Hukumar da ke Kula da ‘Yancin Addini ta Amurka ya yi zargin cewa akwai kusan masu tayar da ƙayar baya masu ɗauke da makamai 30,000 da ke aiki a faɗin Nijeriya.
Rahoton na watan Mayun 2026 mai taken “Masu Take ‘Yancin Addini da Ba na Gwamnati ba a Nijeriya: Mayaƙan Fulani,” ya bayyana cewa waɗannan mayaƙa, waɗanda ke aiki a ƙungiyoyi masu mambobi tsakanin mutum 10 zuwa 1,000, sun zama daga cikin mafi haɗarin masu tayar da tarzoma da ke haddasa take ‘yancin addini a Nijeriya.
A cewar rahoton, hare-haren da waɗannan masu ɗauke da makamai ke kaiwa sun ƙara tsananta rashin tsaro a yankin Middle Belt da kuma kudancin ƙasar, inda suka yi sanadiyyar mutuwar dubban mutane, tarwatsa al’ummomi daga muhallansu, tare da ƙara rura wutar rikici tsakanin ƙungiyoyin addinai.
“Rikicin da mayaƙan suka haddasa ya yi sanadiyyar mutuwar mutane mafi yawa a tsakanin dukkan al’ummomin addini a Nijeriya cikin shekarar da ta gabata idan aka kwatanta da hare-haren ƙungiyoyin ‘yantawaye da kuma ƙungiyoyin masu aikata laifi,” in ji rahoton.
Hukumar ta ce yawancin hare-haren na kai wa al’ummomin Kirista ne hari, ko da yake al’ummomin Musulmi ma sun sha fama da farmaki, kashe-kashe da kuma sace mutane.
Rahoton ya ce duk da cewa waɗannan ƙungiyoyi ba su da shugabanci guda ɗaya, hukumar USCIRF ta bayyana cewa wasu daga cikinsu suna haɗa kai da ƙungiyoyin ‘yanbindiga da kuma ƙungiyoyin masu tsattsauran ra’ayi.
Rahoton ya ƙara da cewa:
“Waɗannan masu ɗauke da makamai suna aiki a yanayi daban-daban tare da manufofi da dalilai iri-iri.
“Duk da cewa da yawa daga cikinsu suna kai hare-hare ne da kansu, wasu kuma lokaci-lokaci suna haɗa kai da wasu ɓangarori daban-daban, daga ƙungiyoyin ‘yanbindiga masu neman kuɗi har zuwa sanannun ƙungiyoyin ta’addanci masu ɗauke da fassarar Musulunci ta tashin hankali.”
Hukumar ta lura cewa mayaƙan sukan kai hari kan ƙauyukan karkara masu rauni da daddare ta amfani da babura, bindigogi masu sarrafa kansu da adduna.
“Sukan riƙe adduna kuma su kutsa cikin al’ummomi masu rauni cikin dare, suna haifar da tsoro domin tilasta wa jama’a barin yankunansu cikin gaggawa da kuma samun iko kan ƙasashen da suke nema,” in ji rahoton.
USCIRF ta bayyana cewa hare-haren mayaƙan sun raba aƙalla mutane miliyan 1.3 da muhallansu a yankin Middle Belt, inda aka tilasta wa da yawa zama a sansanonin ‘yan gudun hijira masu cunkoso da rashin wadataccen tsafta da tsaro.
Rahoton ya kuma tattara bayanai kan sace-sacen mutane da suka shafi majami’u da masallatai.
Hukumar ta ƙara da cewa: “Wasu masu sa ido sun yi hujjar cewa matsalolin muhalli da tattalin arziki ne suke haddasa ayyukan tashin hankalin mayaƙan.”
















