Wa ke da alhakin cutuwar yara sakamakon amfani da kafafen sada zumunta na intanet?
A duk faɗin duniya, gwamnatoci na ɗaukar matakai don sanya dokokin amfani da shafukan sada zumunta ga yara / AP
Wa ke da alhakin cutuwar yara sakamakon amfani da kafafen sada zumunta na intanet?
A fadin kasashe tun daga Turkiyya zuwa Australia, sabbin sauyin dokoki na bayyana ra’ayin bai daya na cewa sanya idanun iyaye kadai ba zai iya kare cutuwar yara daga kafafen sada zumunta na yanar gizo ba.
6 awanni baya

Yunkurin da ake yi na daidaita amfani da shafukan sada zumunta na yara a duniya yana dauke alhaki daga ikon iyaye zuwa shafukan da aka tsara don cin gajiyar hankulan yara.

A duk faɗin duniya, yayin da gwamnatoci ke ɗaukar matakai don sanya dokokin amfani da shafukan sada zumunta ga yara, muhawarar da ake yi game da cutar da shafukan ke yi ga yaran na fuskantar sauyi mai muhimmanci.

Daga Australia zuwa Birtaniya da kuma daga Norway zuwa Turkiyya, dokokin da ake samarwa a ƙasashe da yawa sun taru a kan abu ɗaya: ba za a iya kawar da illolin da amfani da shafukan sada zumunta na yara ke haifarwa ta hanyar sanya idanu da kulawar iyaye kawai ba.

Dole ne a raba alhakin tare da shafukan sada zumuntar waɗanda ke tsarawa, sarrafawa, da kuma cin gajiyar shafukan yanar gizo.

Wannan sauyi ba wai yana wanke iyaye ko hukumomin gwamnati daga nauyin da ke kansu ba ne. Iyalai da kasashe sun kasance manyan masu ruwa da tsaki wajen kare yara.

Duk da haka, gwamnatoci yanzu suna ɗaukar wani matsayi mai haske da nacewa kan cewa ya kamata a miƙa alhakin ga kamfanonin da ke tsara wa, inganta wa, da kuma tallata shafukan sadarwar.

Kamar sauran masu amfani, yara ba wai kawai suna "amfani" da kafofin sada zumunta ba ne, a’a ana ci gaba da j musu gora, ana ƙarfafa musu, kuma ana ci gaba da kula da su a shafuka da manhajoji ta hanyar kayayyakin more rayuwa da aka inganta don haɓaka samun riba.

Hanyoyin sauya allo marasa iyaka, tsarin algorithm, da tagomashi an tsara su da gangan don dorewar tattalin arzikin jan hankali.

A ƙarƙashin waɗannan yanayi, tsammanin iyaye su zama su kadai ne masu tsawatarwa da kuma magance injunan tattalin arziki na tiriliyoyin daloli ba gaskiya ba ne kuma ba adalci ba ne.

Wani bincike mai zurfi na ilimi kan yara da matasa ya nuna cewa yawan amfani da kafofin sada zumunta yana janyo matsalolin damuwa, baƙin ciki, matsalolin barci, ƙarancin hankali, rashin lafiyar jiki da ke da alaƙa da abubuwan gani da aka tantance, da matsalolin cin abinci.

Jari hujjar sanya idanu

Manufar Shoshana Zuboff ta "tsarin sa ido kan jari-hujja" tana ba da tsari mai ƙarfi don fahimtar dalilin da ya sa alhakin ke koma wa zuwa sama.

Shafukan sada zumunta na zamani cikin tsari na tattarawa da nazarin halayen masu amfani, suna hasashen ayyukan da za su yi nan gaba, kuma suna samun kuɗi daga waɗannan fahimta ta hanyar talla da kula da ɗabi'ar masu amfani.

A cikin wannan tsarin, yara ba wai kawai masu amfani da ke da rauni ba ne, har ma da kasancewa masu amfani da bayanai masu muhimmanci.

Kowane duba, dakatarwa, nuna so, da kuma amsawar motsin rai yana haifar da wuce gona da iri na ɗabi'a.

Ga yara waɗanda ci gaban fahimta da motsin ransu har yanzu ke ƙaruwa, wannan cire bayanai yana haifar da sakamako mai zurfi da na dogon lokaci.

Algorithms ba wai kawai suna koyon abin da yara ke so ba; suna kuma tsara abin da za su so.

Saboda wannan dalili, ƙa'idodin yanzu suna ƙara nufin sanya iyaka kan tattara bayanai daga yara, hana tallan da aka yi niyya, suna buƙatar bayyana gaskiya a cikin tsarin shawarwari, da kuma sanya takunkumi kan salon gine-gine da ke haɓaka mu’amala.

Mallake fasahar kere-kere

Ra'ayin Yanis Varoufakis na "fasaha" yana ba da hangen nesa mai kyau don fahimtar wannan rashin daidaiton mallakar.

Shafukan sada zumunta suna ƙara kama da mallakar mulkin mallaka maimakon kamfanonin jari-hujja na gargajiya.

Masu amfani ba su mallaki waɗannan wurare na sadarwa ba; maimakon haka, ana ba su damar shiga sharuɗɗa a ƙarƙashin ƙa'idoji waɗanda masu shafukan suka ƙayyade su kaɗai.

Yara suna girma a cikin waɗannan yanayin da wasu su kadai ke juyawa.

Mu'amalarsu, lokacin hutunsu, da kuma ƙwarewar iliminsu da yawa ana tsara su a cikin tsarin da ba a san shi ba wanda algorithms ke jagoranta maimakon kula wa ta hanyar dimokuradiyya.

A cikin wannan yanayi, ikon iyaye yana da rauni wajen gogayya da ikon algorithm mai ci gaba, wanda ba a gani, kuma mai girma.

Daga wannan mahangar, zargin iyaye kamar sanya bayin ƙasa su ɗauki alhakin yanayin mallakar gidan sarauta ne.

Kasashen da suka fahimci rashin daidaiton iko suna ƙara mayar da hankalinsu daga "bayii" zuwa "iyayen gida".

Hana amfani da kafofin sada zumunta a Australia ga waɗanda ba su kai shekara 16 ba, wanda ya fara aiki a ranar 10 ga Disamban 2025, ya zama ɗaya daga cikin misalan da aka fi gani na wannan sauyi.

Tare da ƙarancin keɓancewa, kamar YouTube Kids, ana buƙatar manhajoji da shafuka su aiwatar da tsauraran matakan tantance shekaru; rashin yin hakan zai janh=yo musu biyan tarar dala miliyan 32.

Tsokacin shugaban kamfanin Meta Stephen Scheeler da ke cewa kamfanin zai iya samun wannan adadin cikin ƙasa da sa'o'i biyu ya haifar da tambayoyi masu muhimmanci game da tasirin irin waɗannan hukunce-hukuncen.

A Birtaniya, Dokar Kariya a Yanar Gizo ta ba wa hukumar kula da kafofin watsa labarai ta Ofcom ikon cin tarar kamfanoni har zuwa kashi 10 cikin ɗari na yawan kudaden kasuwancinsu a duniya.

Firaminista Keir Starmer, da sauran masu ruwa da tsaki a harkokin siyasa da dama, sun bayyana a fili cewa yawan lokacin kallon na’urar waya ko kwamfuta na barazana ga lafiyar yara.

Shawarwarin da Majalisar Tarayyar Turai ta yanke na sanya mafi ƙarancin shekaru 16 don amfani da shafukan sada zumunta da kuma 13 ga abubuwan kirkirarriyar basira da manhajojin bidiyo na bayyana wannan yanayin.

Yayin da Faransa ke muhawara kan haramci gaba ɗaya ga yara 'yan ƙasa da shekara 15 da kuma wani nau'in "dokar takunkumin yanar gizo," Spaniya tana shirya ƙa'idoji da ke buƙatar izinin iyaye ga masu amfani ‘yan ƙasa da shekara 16.

A halin yanzu, Norway ta fahimci rashin ingancin takunkumin da ake da shi a yanzu kuma tana haɓaka ingantattun hanyoyin kulawa.

A Amurka, ƙa'idar shekaru 13 da ke mai da hankali kan sirrin bayanai har yanzu tana nan, amma ƙa'idoji masu tsauri na matakin kasa suna fuskantar ƙalubalen shari'a akan 'yancin faɗar albarkacin baki.

China ta yi amfani da ɗaya daga cikin ƙa'idojin sarrafa yanar gizo mafi tsauri ga yara. Duk da cewa an sanya iyaka ta lokacin amfani na minti 40 ga yara 'yan ƙasa da shekara 14, damar shiga yanar gizo ta kasance gaba ɗaya tsakanin ƙarfe 10:00 na dare zuwa 6:00 na safe agogon kasar.

Duk da cewa TikTok yana da masu amfani da shi sama da rabin biliyan a duk duniya, yana aiki a China a ƙarƙashin wata siga ta daban mai suna Douyin, wadda ke amfani da algorithms daban-daban kuma tana mayar da hankali kan abubuwan da ke yada ilimi.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya bayyana a fili cewa yayin da China ke amfani da TikTok don raunata hankalin yara a duk duniya, tana jagorantar 'ya'yanta ta hanyar Douyin tare da ƙarin ilimi da abubuwan da suke mafi dacewa.

Wannan bambanci ya nuna cewa shafukan kafofin watsa labarun ba wai kawai suna aiki a matsayin kamfanonin kasuwanci ba ne, har ma da kayan aikin yada al'adu.

Gaskiyar cewa an haramta manhajojin kafofin watsa labarun Yammacin duniya a China ya ƙara nuna cewa kasashe suna ƙara kallon shafukan dijital ba a matsayin masu cin kasuwa mai 'yanci ba, har ma a matsayin ababen more rayuwa na dabaru.

Manyan Kamfanoni da zagwanyewar dabi’a

Duk da cewa manyan kamfanonin fasaha da aka fi sani da ‘Big Tech’ sun aiwatar da waɗannan matakan, har yanzu suna adawa da irin waɗannan takunkuman.

Bayan gabatar da haramcin, Firaministan Australia Anthony Albanese ya bayyana cewa an toshe tare da goge, ko kuma takaita shafukan kafofin sada zumunta sama da miliyan 4.7 mallakar masu amfani 'yan ƙasa da shekara 16.

Wakilan kamfanonin ‘Big Tech’ sun yi jayayyar cewa fasahar tantance shekaru tana barazana ga sirri, tana keta haƙƙin yara, kuma tana iya rage amincin intanet.

Duk da haka, waɗannan ƙorafe-ƙorafe galibi suna ɓoye damuwa mai zurfi: hatsarin rasa tushen masu amfani mai riba wanda ke samar da bayanai kyauta da kayan amfani.

Shugaban Meta Mark Zuckerberg, shugaban Instagram Adam Mosseri, da shugaban Snapchat Evan Spiegel za su fuskanci shari'a bisa zargin cewa sun tsara abubuwa da ke sanya maita da jaraba ga masu amfani.

A halin yanzu, alƙawarin son rai kan ɗabi'a da aminci yana kama da abin da za a iya kwatantawa da "zagwanyewar dabi’a": yaɗuwar alhakin ba tare da canza tsarin kasuwanci na asali ba.

Manufofin kare yara a Turkiyya

Muhawara game da kasancewar yara a kan yanar gizo a Turkiyya ta nuna yanayin da ake ciki a yankin, amma galibi sun yi daidai da yanayin ƙa'idoji na duniya.

Wani daftarin rahoto mai taken "Barazana da Hatsarin da ke Jiran Yaranmu a Duniyar yanar Gizo," wanda Kwamitin Kula da Haƙƙoƙin Yara na Kwamitin Kare Haƙƙoƙin Ɗan Adam na Majalisar Dokokin Turkiyya ya shirya, ya bayyana tsarin wannan hanyar.

Rahoton ya haɗa da shawarwari kamar hana yara ‘yan kasa da shekaru 18 amfani da yanar gizo da daddare, sannan a haramtawa ‘yan kasa da shekaru 15 amfani da shfukan sadarwa, a takaita wa makarantu amfani da manhajojin, a karfafa kula da shiryarwa da kuma samar da sim card na waya na musamman ga yara.

Ministar Iyali da Ayyukan Jama'a Mahinur Ozdemir Goktas ta sanar da cewa nan ba da jimawa ba za a gabatar da shirye-shiryen dokoki amfani da kafofin sada zumunta da suka shafi yara 'yan ƙasa da shekara 15 a gaban Majalisa.

Dalilin da ya sanya kawo ƙa'idar ya haɗa da ƙaruwar matakan baƙin ciki, damuwa, matsalolin halayya, da hatsarin hulɗa da cibiyoyin aikata munanan laifuka a kafofin sadarwa na zamani na yanar gizo.

Minista Goktas ta bayyana cewa ba za a ɗauki yara a matsayin albarkatun kasuwanci ko wuraren tattara bayanai na manhajojin sada zumunta ba. Maimakon samar da wani shiri na hana 'yancin faɗar albarkacin baki, an gabatar da waɗannan matakan a matsayin wata manufa ta gwamnati mai muhimmanci da nufin kare yara daga hatsarin yanar gizo.

A cikin wannan tsari, manhajar "Cocuklar Guvende" (Yara Suna da Kariya) ana ba da jagoranci da hanyoyin samun bayanai ga yara da iyaye.

Hukumomin musamman sun jaddada cewa yaƙi da abubuwan da ke cutarwa dole ne ya zama fifikon manhajoji da kamfanoninsu za su aiwatar, maimakon dogaro da hanyoyin magancewa bayan matsala ta faru.

Ba yara kaɗai ba ne ke fuskantar barazanar shfukan sadarwa na yanar gizo. Manya waɗanda ba su da ilimin zamani, musamman tsofaffi, suna ƙara zama masu rauni ga bayanan karya, rarrabuwar kawuna, da ayyukan yaudara ta hanyar amfani da algorithmic.

Saboda haka, ƙa'idar kula da manhaja ba kawai matakin kare yara ba ne.

Hakan kuma gwagwarmaya ce don tsarkake yanayin jama'a da yake tattare da yanar gizo daga bayanan karya, don 'yantar da hanyoyin dimokuradiyya daga kamen algorithmic, da kuma kiyaye haɗin kai tsakanin jama'a.

Idan manhaja ko kamfani suka tsara yanayin amfani da su a yanar gizo, horarwar algorithms, da kuma riba cikin tsari daga tattalin arzikin jan hankali, ba za a dora alhaki a kan daidaikun mutane, iyali ko zabin mai amfani ba,

Dole ne a raba alhakin, kuma dole ne a kawo iko ƙarƙashin kulawar jama'a baki daya.