Nijeriya: An haramta wa 'yan ƙabilar Igbo naɗin sarautar gargajiya a ƙasashen waje
An gudanar da taron Ohaneze Ndigbo a ranar 9 ga Afrilu a birnin Enugu. Bianca Ojukwu/X / TRT Afrika English
Nijeriya: An haramta wa 'yan ƙabilar Igbo naɗin sarautar gargajiya a ƙasashen waje
Haramcin, wanda aka sanar a ranar 9 ga Afrilu a birnin Enugu da ke Nijeriya, ya yi nuni kan yadda naɗin 'sarakunan' Igbo a ƙasashen waje ke yin mummunan tasiri ga martabar Njeriya da kuma dangantakarta a fannin diflomasiyya.

An haramta wa 'yan ƙabilar Igbo nada muƙaman sarautar "gargajiya" a wajen Nijeriya.

Matakin hakan ya biyo bayan takaddamar da ta barke kwanan nan kan nadin "Sarkin Igbo" a ƙasar Afirka ta Kudu, wanda ya haifar da tashin hankali a tsakanin 'yan Afirka ta Kudu.

Yanzu haka ƙungiyar al'adu da zamantakewa ta al'ummar ƙabilar Igbo a faɗin duniya, Ohaneze Ndigbo ta sanar da matakin haramta duk wani naɗi na sarauta a ƙasashen waje, Matakin da gwamnatin Nijeriya ta goyi baya.

Karamar Ministar Harkokin Waje ta Nijeriya Bianca Odumegwu-Ojukwu, wacce ta halarci taron babban taron Ohaneze inda aka yanke shawarar a ranar 9 ga Afrilu a birnin Enugu, ta ce "abin bakin ciki ne ganin yadda naɗin muƙaman sarautar 'gargajiya' na al’ummar Igbo a ƙasashen waje" ya yi mummunan tasiri ga mutuncin Nijeriya da dangantakar diflomasiyya.

Bianca Odumegwu-Ojukwu, wacce ita ma 'yar kabilar Igbo ce, ta ce a lokuta da dama al'ummomin da ke karɓar baƙi suna kallon naɗa sarakunan gargajiya a ƙasashen waje "a matsayin cin zarafi".

‘Yanayi na rashin Mutunci’

Ta ƙara da cewa "almubazaranci" da "nuna isa da 'yan Nijeriya ke yi" a lokacin irin waɗannan bukukuwa na nadin sarauta, a wasu lokuta yana cin karo da yanayin ƙalubalen tattalin arziki da 'yan ƙasashen da ke karɓar baƙuncinsu ke ciki wanda kuma ‘‘bai dace ba.’’

Ministar ta ce za a sanar da ofisoshin jakadancin Nijeriya da ke ƙasashen waje da kuma hukumomin ƙasashen game da matakin haramcin da aka dauka don tabbatar da bi ƙa'idoji da kuma yiwuwar sanya takunkumi ga waɗanda suka take dokar.

Duk da cewa al'ummomin Igbo da ke ƙasashen waje suna da 'yancin nuna al'adunsu, a cewar ministar ya na da ƙyau su yi la'akari da yanayin al'ummomin ƙasashen da ke karɓar baƙuncinsu.

A cikin wata sanarwa da ta fitar, Bianca Odumegwu-Ojukwu ta ce ana iya kiran shugabannin al'ummomin Igbo da ke ƙasashen waje da "Onyendu" wanda ke nufin shugaba maimakon "Igwe" ko "Eze" da ke nufin sarki.

Matakin haramcin na zuwa ne kusan wata guda bayan da aka naɗa wani ɗan Nijeriya, Cif Solomon Ogbonna Eziko, a matsayin "Igwe Ndigbo Na Gabashin London", wato "sarkin ƙabilar Igbo na Gabashin London," wani birni a lardin Gabashin Cape na Afirka ta Kudu

Lamarin ya haifar da tashin hankali daga mazauna yankin da hukumomin Afrika ta Kudu, waɗanda suka ɗauke hakan a matsayin "rashin girmamawa" ga dokoki da al'adun Afirka ta Kudu.

Daga baya Nijeriya ta nemi afuwa, inda jami'an diflomasiyyar ƙasar suka yi ƙoƙarin warware matsalar.

Kazalika an taba makamancin irin wannan yanayin a Ghana a shekarar 2024 lokacin da al'ummar Igbo da ke can suka gudanar da bikin naɗin sarauta a Accra don naɗa "Eze Ndi Igbo Ghana", ma'ana "Sarkin ‘yan kabilar Igbo a Ghana," yanayin da ya fusata 'yan Ghana.

'Yan ƙabilar Igbo suna ɗaya daga cikin manyan kabilu a Nijeriya, galibi daga kudu maso gabashin ƙasar, kuma suna da al'umma a ƙasashen waje da yawa, waɗanda aka fi sanin su da yin kasuwanci.