Yadda Harsuna 2,000 suka sa Afirka ta zama nahiya mafi yalwar lugga a duniya
A duk fadin duniya, kusan harsuna tara suna bacewa kowace shekara. Wato, harshe daya kowace kwana arba'in. / Others
Yadda Harsuna 2,000 suka sa Afirka ta zama nahiya mafi yalwar lugga a duniya
Nijeriya kaɗai na da fiye da harsuna 520, sannan a faɗin nahiyar Afirka akwai harsuna 428 da ke cikin haɗarin ɓacewa sakamakon raguwar masu magana da harsunan.
24 Fabrairu 2026

Babu wata nahiyar da ta zo kusa da Afirka a yawan gadon harsuna karin harshe da suka kai fiye da 2,000. Wannan adadi ya kai kusan kashi ɗaya cikin uku na duka harsunan da ake magana da su a duniya.

Amma yayin da duniya ke tunawa da Ranar Harshen Uwa ta Duniya a ranar 21 ga Fabrairu, wannan murna ta zo da tambaya mai ɗaci: nawa ne daga cikin waɗannan harsunan za su tsira?

Ethnologue, wani shafin kundin bayanai kan harsunan da ake amfani da su a duniya, ya bayyana cewa kusan kaso 44 cikin 100 daga cikinsu yanzu suna cikin haɗari, inda aka ƙiyasta cewa kusan harsuna 428 a Afirka na fuskantar barazanar ɓacewa.

A duniya gaba ɗaya, kusan harsuna tara suke ɓacewa a duk shekara. Wato harshe ɗaya duk bayan kwanaki 40.

"Idan waɗannan harsuna suka mutu, ilimin da suke ɗauke da shi zai mutu tare da su," in ji Leonard Muaka, shugaban sashen harsuna da al'adun duniya a Jami'ar Howard a Amurka, a wata mahawara da aka shirya a daidai lokacin tunawa da ranar.

Akwai tarurruka da dama a wannan makon – daga tarukan al'umma a ƙauyukan Kenya, zuwa tarukan ilimi a Washington DC – inda aka mayar da hankali kan ƙasashen da suka fi yawan harsuna a duniya.

Bayanan da shafin yanar gizo na Statista ya tattara sun jera ƙasashen Afirka bisa yawan harsunan masu rai a cikinsu, kuma labaran da ke tattare da waɗannan ƙididdigar sun bambanta kamar yadda harsunan kansu suka bambanta.

Wadda ke gaba a cikin jerin ita ce ƙasar da ke da kusan kashi ɗaya bisa huɗu na harsunan da ake magana da su a nahiyar, wato Nijeriya.

Ƙarfin harshe

Sakamakon tana da fiye da harsuna 520, da yawan jama'a miliyan 223, Nijeriya ita ce babban sansanin harsuna mabambanta a Afirka ba tare da gardama ba. Ingilishi shi ne harshen hukuman, amma rediyo da talabijin suna yin Hausa a arewa, Yarabanci a kudu maso yamma, Igbo a kudu maso gabas, da sauran ɗaruruwan harsuna, ciki har da Fulfulde, Ibibio, Kanuri, da Tiv.

Wata alamar kasancewa ɗan Nijeriya ita ce zama mai magana da harsuna da dama — kana iya sauyawa tsakanin harshen uwa, da harshen maƙwabta, da kuma wanda ka gada daga masu mulkin mallaka.

Kamaru na biye da Nijeriya, da harsuna 227, inda ake kwatanta ta da “ƙaramar Afirka” saboda bambancin ƙasa da al'adu. Faransanci da Ingilishi na fafatawa wajen ɗaukakar matsayi, kuma ‘yar tafiya ta ‘yan mintuna takan iya kai ka ga ƙetare iyakoki.

Al’ummar ƙasar sun fi magana da Fulfulde, Ewondo, da Duala a manyan yankunan Kamarun. Amma ƙasar tana ƙunshe da harsuna masu ƙarancin yaɗuwa. Daga cikin waɗannan akwai Gyele, wanda ɗaruruwan mafarauta ke amfani da shi a dazukan bakin teku. Akwai Bung, harshe da ke fuskantar ɓacewa saboda masu magana da shi sun yi ƙasa da 30 a ƙauye guda kacal.

Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo, ita ce ƙasa ta biyu mafi girma a Afirka fannin faɗi, kuma tana da harsuna 214. Mutanen ƙasar na mu'amala a kullum da Lingala, Swahili, Kikongo, da Tshiluba, da sauran ɗaruruwan harsuna.

Harsunan masu rauni

Harsunan hukuma a Chadi su ne Faransanci da Larabci, amma abin ya bambanta a zahiri.

Jama’ar ƙasar na magana da fiye da harsuna 100 na asali. Larabcin Chadi na aiki a matsayin harshen haɗin-gwiwa don kasuwanci da mu'amala ta yau-da-kullum tsakanin ƙabilu, yayin da Sara ya mamaye yankin kudu. A gefe akwai harsuna kamar Kujarge, wanda mutane 'yan dubu kaɗan ke magana da shi kusa da iyakar Sudan, da Bedjond, wanda ke fuskantar ƙaruwar barazana yayin da matasa ke komawa harsuna masu rinjaye.

Tanzania na da harsuna 128, amma Swahili ne ke matsayin harshen ƙasa da ke haɗe al’umma. Ana amfani da shi a siyasa da ilimin firamare. Ingilishi na nan a matsayin harshen makarantu na sakandare da manyan kotunan shari'a, yayin da harsunan asali kamar Sukuma da Chagga suke da miliyoyin mutane masu magana da su.

Ƙasar kuma na da harsuna da ke cikin haɗari sosai kamar Akie, wanda mafarautan da adadinsu ke raguwa suke magana da shi. Akwai Dahalo, harshe da ke da masu magana suke ƙasa da 500, wanda kuma yake da salon sauti na daban da ba a saba ji ba.

Harsuna 92 na Habasha (Ethiopia) galibi masu dangi da reshen Afroasiatic, inda Oromo da Amharic suke matsayin manyan harsunan aiki na tarayya. Somali da Tigrinya su ne manyan harsunan yanki. A ɗayan gefen akwai harsuna kamar Ongota, wanda ke cikin mawuyacin hali a kudu amso yamma na Habasha, wanda ke da tsofaffi kaɗan masu magana da shi. Sai kuma Komo, wanda ƙananan al'ummomi a gefen iyakar Sudan ke amfani da shi.

Afirka ta yamma

Faransanci shi ne harshen hukuma a Ivory Coast, ko da yake Dioula na aiki a daidaitaccen tsari da kuma tsarin harshen kasuwanci tsakanin ƙabilu. Baoulé yana daga cikin harsunan asali mafi yawan masu magana a yankunan tsakiya.

Harsuna 88 na ƙasar sun haɗa da harsuna masu haɗari sosai, kamar Eotile a bakin teku, da Mbre, wani harshe mai zaman-kansa wanda ƙananan al'umma a tsakiyar ƙasar ke amfani da shi ba tare da dangoginsa na harshe da aka sani ba.

Ghana na da harsuna 83, waɗanda Turanci ke jagoranta a matsayin harshen hukuma. Harsunan Akan – Twi da Fante – su ne mafi girman harsunan asali a kudu, yayin da Dagbani da Ewe suka mamaye arewa da gabas bi-da-bi.

Akwai harsuna kamar Dompo, wanda ƙasa da mutane dubu ɗaya ke magana da shi a yankin Brong‑Ahafo, da Animere, wanda ƙasa da mutane 700 ke magana da shi a gefen iyakar Togo, duka suna fuskantar makoma mai rauni.

Yankunan Nilu

Harsuna a Sudan sun samu tasiri daga Larabci, wanda ake magana da shi a cikin tsari na zamani da kuma kari-kari na gida. Tare da shi akwai Ingilishi, wanda ke da muhimmanci a harkokin ilimi da gwamnati.

Harsuna 75 na ƙasar sun haɗa manyan harsunan asali kamar Beja a gabas, da harsunan Nubian a bakin kogin Nilu, da wasu harsuna keɓaɓɓu kamar Midob, wanda ƙananan al'umma a Darfur ke magana da shi, da Tima, wanda aka ayyana a matsayin mai haɗarin ɓacewa a Dutsen Nuba.

Sudan ta Kudu, ƙasa mafi ƙarancin shekaru a jerin, ta zaɓi Ingilishi a matsayin harshen hukuma bayan samun 'yanci, don nisantar tasirin Larabci na arewa. Amma harsuna 73 na ƙasar suna ba da labari daban.

Dinka da Nuer su ne manyan harsuna, miliyoyin mutane na magana da su , yayin da ɗaruruwan ƙananan harsunan al'umma, ciki har da Shilluk da Bari, ke wanzuwa tare da wasu harsuna masu rauni kamar Tennet, da mutane 'yan dubunnai ke magana da shi a kudu, da Indri, wanda 'yan ƙarni ɗari kaɗan ke magana da shi kusa da iyakar Uganda.

A duk waɗannan ƙasashe, ƙididdigar asarar harshe tana bayyana a giɓin da ke tsakanin manyan harsuna da ƙananan tsofaffi masu magana da harshen, waɗanda ke kiyaye ƙamusin kalmomi rayayyu.

Ranar Harshen Uwa ta Duniya tana sanya wata rana a kalanda, don murnar wanzuwar harsunan. Abin da ranar ba za ta iya cimmawa ba shi ne dakatar da tasirin lokaci kan harsunan duniya.