Rikicin da ya shafi dangin marigayi mawaƙin Nijeriya Mohbad ya ɗauki wani sabon salo.
A yanzu haka ana sa ran gudanar da gwajin kwayoyin halitta na DNA a Amurka da Birtaniya a makonni masu zuwa don tantance sahihancin ko Liam ɗan Mohbad ne.
Mahaifin Mohbad, Joseph Aloba, ya shigar da ƙara a kotu a shekarar 2025 don tabbatar da cewa mawaƙin Afrobeats ɗin shine uban asalin yaron na asali.
Yanzu haka lamarin ya keta hazo, inda wata kotu a jihar Legas ta amince a gudanar da gwaje-gwaje a wurare uku dake ƙasashen waje - ɗaya a Amurka yayin da biyu kuma a Birtaniya - duk don a gudanar da gwajin DNA a ƙoƙarin warware takaddamar da ke tsakanin mahaifin Mohbad da matarsa, Omowunmi.
Hukuncin, wanda Alkali Adefisoye Sonuga ya yanke a ranar 27 ga Fabrairu, a cewar rahotanni daga kafofin watsa labarai na cikin gida, ya zo ne bayan da dukkan ɓangarorin suka amince kan buƙatar a yi gwajin DNA.
Ko da yake Omowunmi ba ta fito fili ta yi tsokaci game da wannan sabon hukunci ba.
Sai dai, mahaifin Mohbad ya ce ya "yi farin ciki" da hukuncin kotun, yayin da kafofin watsa labarai na cikin gida suka ambato lauyansa, Oladayo Ogungbe, yana cewa sun kafe kan yin gwaje-gwaje a ƙasashen waje saboda wuraren da ake da su a Nijeriya ba su da kayan aikin yin "gwajin na alaƙar wani sassan jiki.’’
An dakatar da binne mawaƙin
Ogungbe ya bayyana cewa matar mawaƙin da mahaifinsa sun zaɓi dakin gwaje-gwaje guda ɗaya kowannensu don gudanar da gwajin, yayin da kotun ta zaɓi wani wurin gwaji mai zaman kansa.
"Dole sakamakon uku su fito iri ɗaya," a cewar Ogungbe.
Kazalika kafofin watsa labarai na cikin gida sun ba da rahoton cewa, ana sa ran tattara samfuran DNA ɗin a watan Afrilu a gaban dukkan ɓangarorin.
An haifi yaron da ake magana a kai, Liam, 'yan watanni kafin mutuwar Mohbad a watan Satumba na 2023 bayan ya yi fama da wani ɗan gajeren jinya yana da shekaru 27.
Takaddama game da sahihancin kasancewar Mohbad uban yaron na asali ya dakatar da shirye-shiryen binne mawaƙin, wanda ainihin sunansa shine Ilerioluwa Oladimeji Aloba, da zuwa yanzu ya shafe shekaru biyu da mutuwa.
Rahotanni sun ce takaddamar ta ta'allaka ne kan raba gadon kadarorin mawaƙin, ko da yake ba a fayyace ainihin abin da ya bari ba.
Mutuwar mawaƙin wanda ya rera waƙar "Feel Good" da "KPK" ya kasance batun ce-ce-ku-ce da kawo yanzu ba a warware ba.
Yayin da aka wanke Naira Marley da abokinsa Sam Larry da hannu a cikin mutuwar Mohbad a bara, masu gabatar da ƙara na Jihar Legas suna ci gaba da tuhumar wata ma'aikaciyar jinya da wani abokin mamacin saboda "rashin kulawa da sakaci" a lafiyarsa.














