An fitar da Rahoton Farin Ciki na Duniya na 2026, inda Mauritius ke kan gaba a cikin jerin ƙasashen Afirka da suka fi yawan mutane dake cikin farin ciki, inda take da maki 5.9 kana ta na matsayi na 73 a duniya.
Ƙasar tsibirin ta ci gaba da ficewa saboda kwanciyar hankalin siyasa, haɗin kai na zamantakewa, da ingancin rayuwa. Libya da Algeria suna kusa da juna, duka suna da maki 5.7 na farin ciki, wanda ke nuna yadda ko a cikin mawuyacin yanayi na siyasa, abubuwa kamar alaƙar al'umma da goyon bayan zamantakewa har yanzu suna taka muhimmiyar rawa a yadda mutane ke kimanta rayuwarsu, in ji rahoton.
Baya ga matsayin Afirka, ƙasashe kamar Mozambique, Gabon, da Côte d'Ivoire sun faɗi cikin matsakaicin matsayi, inda ake daidaita ƙalubalen tattalin arziki ta hanyar tsarin yanayin rayuwa wanda ke taimakawa wajen rage wahalhalu.
Kamaru da Afirka ta Kudu ne ke biye, inda Afirka ta Kudu ke matsayi na 101 a duniya da maki 5.0, yayin da Nijeriya ke ƙasa da matsayi na 106 da maki 4.7.
Shugabannin duniya
Abin da ya fi daukar hankali a wannan yanayin shi ne matsayin Afirkaya sha banbam da sauran ƙasashen duniya, inda kasashe kamar Finland, Denmark da Iceland ke ci gaba da kasance wa akan gaba a jerin matsayin.
Mafi akasari ana danganta nasararsu da samun cibiyoyi masu ƙarfi, da ƙarancin cin hanci da rashawa da kuma tsarin walwalar al’umma, a cewar rahoton.
A ƙasan jerin kasashen kuwa, rahoton ya nuna yadda farin ciki ke da alaƙa da kwanciyar hankali da tsaro. Afghanistan ta kasance ƙasa mafi ƙarancin farin ciki a duniya, inda take da maki 1.4 kawai.
Sai kuma Sierra Leone, Malawi da Zimbabwe, inda matsin tattalin arziki, da rashin tabbas na siyasa da kuma ƙarancin damammakin samun muhimman ayyuka ke ci gaba da haifar da tsaiko a tsarin rayuwa ta yau da kullun.
Yemen da Lebanon suma suna dab da ƙasa, inda suke yawan fama da rikice-rikice da durƙushewar tattalin arziki, in ji rahoton.
Tasirin kafofin sada zumunta
Ɗaya daga cikin abubuwan da suka fi jan hankali a cikin rahoton shine raguwar farin ciki da walwala tsakanin matasa a Arewacin Amurka da Yammacin Turai a cikin shekaru 15 da suka gabata.
Wannan yanayin yana daidai da ci gaban kafofin sada zumunta, rahoton ya ce lamarin ya haifar da tarin tambayoyi game da tasirinsu na tsawon lokaci.
Rahoton ya gano cewa yawan amfani da kafofin sada zumunta - fiye da sa'o'i biyar a rana - yana da alaƙa da matakan damuwa masu yawa, da alamomin ƙunci da kuma ƙaruwar fahimtar matasa na rashin daraja da kuma ganin kimar kansu.
An gina dandamalin kafofin sada zumunta ne bisa ga amfani da abubuwan da ba sa tafiya yadda ya kamata, kamar bibiyar tsararrun hotuna da bidiyo, waɗanda suke da mummunan tasiri a rayuwar al’umma, in ji rahoton.
Bibiyar fitattun ‘yan soshiyal midiya, musamman waɗanda suka shahara a tsakanin matasa, da aka sani da ‘yan Gen Z, suna bayyana salon rayuwa da ake kwaikwayarsu wanda ke haifar da gasa da kuma sanya ƙunci da rashin godiya da abun da mutum yake da shi na samun farin ciki, in ji rahoton.
Ko da yake, ga nahiyar Afirka, jimilar raguwar farin ciki gabaɗaya yana da alaƙa da ƙalubalen tsari da na tattalin arziki fiye da na kafofin intanet.
Cibiyar Bincike ta Wellbeing da ke Jami'ar Oxford ce ta tattara rahoton tare da haɗin gwiwar Cibiyar Samar da Ci Gaba Mai Dorewa ta Majalisar Dinkin Duniya.











