| Hausa
RAYUWA
2 minti karatu
Mata da 'yanmata na cikin mafi munin bala'i da ƙasƙanci a Gaza - MDD
Wata babbar jami'a a UN Women ta bayyana halin da mata da 'yanmata ke ciki a Gaza a matsayin daya daga cikin mafi munin rikicin jinƙai a duniya, inda ta yi kira ga ƙasashen duniya da su dauki mataki.
Mata da 'yanmata na cikin mafi munin bala'i da ƙasƙanci a Gaza - MDD
MDD ta yi gargadin cewa, a kowacce rana mata da 'yan matan Gaza na fama da matsalolin rayuwa kowace rana / AP

Mata da 'yanmata a Gaza na rayuwa a cikin ɗaya daga cikin yanayi mafi munin bala’i jinƙai da ƙasƙanci a duniya, in ji wata babbar jami'ar Majalisar Dinkin Duniya a fannin ayyukan Mata.

Sarah Hendriks, daraktar tsare-tsare da shirye-shirye da kuma tallafin gwamnatoci a MDD, ta ce yanayin rayuwa ya zama gwagwarmaya ta yau da kullum ga mutane da yawa a yankin Falasdinu da Isra’ila ta lalata.

"Mata da 'yanmata a Gaza suna rayuwa ne a ɗaya daga cikin bala'o'i jinƙai da yanayin da ya fi tayar da hankali a duniya, inda rayuwa ta gagari mutane da dama," kamar yadda Hendriks ta shaida wa manema labarai a wani taro a hedikwatar Majalisar Dinkin Duniya da ke New York.

Ta bayyana "goyon baya ga mata da 'yanmata a yankin Gabas ta Tsakiya" a daidai lokacin da ake ci gaba da samun tashin hankali, tana mai jaddada kiran Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres na a dakatar da fadan.

Hendriks ta ce UN Women na aiki tare da ƙungiyoyin da mata ke jagoranta a Gaza don shawo kan mutanen da aka tilasta wa yin gudun hijira, da waɗanda ke fama da matsalar damuwa da kuma rashin tsaro.

"Bukatunsu sun wuce dukkan yanda ake zato. Suna buƙatar mutunci, adalci, abubuwan more rayuwa da kuma rawar da za su taka wajen sake gina makomarsu," in ji ta.

Ta jaddada cewa, dole a hada juriya da jagorancin mata a Gaza da damammaki na jinƙai, da kariya da kuma saka hannun jari na ƙasashen duniya.

Rumbun Labarai
Daga ƙasusuwa zuwa abin kwaɗayi: Orenge, abincin da ke sanya santi a Nairobi
Yadda A-Daidaita-Sahu na mata zalla ke sauya sufuri a jihar Kano ta Nijeriya
Kafafen sada zumunta na da alaƙa da raguwar farin ciki a faɗin Afirka da wasu yankuna - Rahoton 2026
Kuomboka: Ƙayatattun al'adun Masarautar Zambia mai shekara 300
Ƙalubalen sauyin yanayi a Afirka: Asarar rayuka, tafiyar ruwa da gidaje da rashin tabbas
An haifi wasu ‘yanbiyun gwaggwon biri da ke da wuyar samu karo na biyu a Congo DRC
Yadda raguwar kudin tallafi ke kai mutane kabari a Afirka
Yaya kaifin basira da fahimtar tausayi yake tsakanin giwaye?
Lailatul Qadri: Dare guda mai darajar watanni 1,000
Cutar kuturta a Afirka: Yanzu ne lokacin sauya lamarin
Mohbad: Taƙaddama game da ko marigayi mawaƙin Nijeriya shi ne uban ɗansa na asali
Azumi da Ciwon Suga: Shawarwarin ƙwararrun Lafiya ga Musulmai a watan Ramadan
An gano ƙwarangwal ɗin wata babbar dabbar dinosaur mai kama da tsuntsu a Hamadar Nijar
Yadda Harsuna 2,000 suka sa Afirka ta zama nahiya mafi yalwar lugga a duniya
Ramadan a Gaza: Falasɗinawa na kokawa kan yadda yaƙi ya hana su abubuwan da suka saba lokacin azumi
Cibiyar Al’adu ta Yunus Emre ta haɗa Turkiyya da Nijeriya ta hanyar fasaha
Yadda azumin Ramadan ke inganta lafiyar jiki
Dalilan da za su ba lallai a fara azumin Ramadan na 2026 ranar Laraba ba a Nijeriya
Dalilin da ya sa harshenku na asali ke tsara duk wani yare da kuke magana da shi
Dalilin da ya sa har yanzu kuturta ke cikin cututtukan da ke addaba da barazana ga ɗan'adam