Yadda A-Daidaita-Sahu na mata zalla ke sauya sufuri a jihar Kano ta Nijeriya
RAYUWA
3 minti karatu
Yadda A-Daidaita-Sahu na mata zalla ke sauya sufuri a jihar Kano ta NijeriyaShirin ya samar da wani tsari inda direbobi mata ke amfani da A-Daidaita-Sahu don jigilar fasinjoji mata zalla. An haramta wa maza zama direbobi ko fasinjoji a tsarin.
A-daidaita-sahu na Mata Zalla suna da launin ruwan hoda domin a iya gane su cikin sauƙi. / TRT Afrika English
2 awanni baya

An samar da wani tsari na sufuri na musamman ga mata zalla a birnin Kano da ke arewacin Nijeriya, inda mafi yawan al’ummar Musulmai ne, da nufin magance damuwar mata da rashin jin daɗinsu a cikin cunkoson ababen hawa na jama’a.

Shirin wanda ake kira da Mata zalla, yana samar da kekunan A-Daidaita-Sahu inda direbobi da fasinjoji duk mata ne, yayin da aka haramta wa maza shiga ko tuƙawa.

Kano ita ce jiha ta biyu mafi yawan jama'a a Nijeriya baya ga Legas, kuma a tsawon shekaru ta yi ta fama da ƙalubale a tsarin sufurinta.

Yawancin lokuta mata su kan dogara ne da tsarin sufuri na jama'a wanda ya haɗa jinsi daban-daban don zirga-zirgar yau da kullum kamar zuwa kasuwanni da asibitoci.

Ruwan hoda

Yanayin ya kasance abin damuwa a jihar da Musulmai suka fi yawa da kuma a dukkan faɗin yankin.

Duk da cewa galibi ana yi A-Daidaita-Sahu fenti a Kano da sauran sassan Nijeriya da launin rawaya da kore, amma A-Daidaita-Sahun na Mata Zalla suna da launin ruwan hoda ne don sauƙin ganewa da kuma samun haɗin kai a tsakanin mata.

Hajiya Hauwa Ahmad Tarauni ce ta kafa tsarin kuma ita take jagorantar shirin, an ƙaddamar da shi ne shekarar 2024 a ƙarƙashin ƙungiyar agaji ta gida da aka sani da ƙungiyar Mata Zalla Cooperative Society.

Baya ga magance matsalolin tsaro da daidaita al'adun yankin da addininsu, yana kuma mai da hankali kan ƙarfafa tattalin arziki ga mata.

Ya kuma ba da fifiko ga zawarawa da matan da mazajensu suka mutu, inda ake ba su horo wajen iya tuƙi da kuma damar samun kuɗi a fannin sana’ar da maza suka mamaye.

Hajiya Hauwa Tarauni ta shaida wa TRT Afrika cewa an horar da mata sama da 200 zuwa yanzu, kana ana ƙara samun mata da suke zuwa kowace rana don yin rajista a cikin shirin.

Amma saboda "ƙarancin kuɗi," mata 100 ne kawai daga cikinsu suka karɓi A-Daidaita-Sahun a yanzu, waɗanda suke amfani da batura masu amfani da wutar lantarki, in ji ta.

Bashin shekara uku

Ana ba su A-Daidaita-Sahun ne a kan bashi, wanda ake sa ran za su biya a tsawon shekara uku.

"Muna buƙatar ƙarin tallafi saboda ƙarin mata suna zuwa domin su sami abin gudanar da rayuwa," in ji Tarauni.

Shirin yana taimakawa mata tare da ba su damar tallafa wa kansu da 'ya'yansu.

Wasu mutane sun nuna rashin gamsuwa game da shirin, la’akari da cewa ba a saba ganin direbobin tasi na mata ba da yawa a cikin birnin.

Sai dai duk da haka, wayar da kai jama’a da ake yi ta hanyar zuwa gida-gida da kuma watsa shirye-shiryen rediyo suna taimaka wajen ƙara karɓuwar shirin.

Masu gudanar da shirin sun ce tallafin saka hannun jari mai yawa daga mutane masu zaman kansu da hukumomi na iya taimakawa wajen faɗaɗa aikin, wanda suke ganin zai iya amfanar da mata a faɗin Nijeriya waɗanda ke fuskantar makamancin irin waɗan ƙalubalen.