Cutar kuturta a Afirka: Yanzu ne lokacin sauya lamarin
RAYUWA
3 minti karatu
Cutar kuturta a Afirka: Yanzu ne lokacin sauya lamarinIyalin mai cutar kuturta kan samu ƙyama duk da cewa ana iya warkewa daga cutar, sannan waɗanda suka warke ba sa barazanar yaɗa ta. Don haka hana tsangwama yana da muhimmanci tamkar na bincike da magance ta.
A 2024, an samu faruwar cutar kuturta fiye da 19,000 a yankunan Afirka

Daga Dorothy Achu

A 2026, bai kamata cutar kuturta a ce tana kawo cikas ga rayuwa ba. Muna da hanyoyin gano ta da wuri, da magance ta da kyau, da kawar da nakasar da take iya haddasawa. Amma duk da haka tana ci gaba da shafar dubban mutane a Afirka.

Wannan tazara tsakanin abin da muka sani da abin da ke faruwa har wa yau a zahiri, hujja ce ta cewa wajibi mu tashi tsaye kan lamarin.

Nan da ‘yan kwanaki, ofishin Hukumar Lafiya ta Duniya a Brazzaville zai karɓi baƙuncin taro kan kawar da kuturta. Wannan zai zama babbar dama ga Afirka ta yi nazari kan batutuwan lafiya da zamantakewa da ke hana cigaba, da kuma samar da mafita kan cutar da ke haifar da ƙyama tsakanin mutane.

A 2024, an samu faruwar cutar kuturta fiye da 19,000 a yankunan Afirka. Cikinsu akwai yara, wanda ke nuni a fili cewa cutar na ci gaba da yaɗuwa.

Da yawan mutane na jinkirin neman magani, har sai lokacin da nakasa ta fara bayyana a zahiri. Cutar kuturta tana ci gaba da zama mai alaƙa da rashin daidaiton jama’a wajen samun kiwon lafiya, da wayar da kai, da kariyar jama’a.

Baya ga tasirinta a fannin lafiya, cutar kuturta na ci gaba da haddasa wa mutane da dama tsangwama. A wasu al’ummomin, tsoro da canfe-canfe suna janyo ƙyama, rasa aiki, da hana zuwa makaranta.

Gabaɗaya iyalin mai cutar kuturta kan samu ƙyama, duk da cewa ana iya warkewa daga cutar, sannan waɗanda suka warke ba sa barazanar yaɗa ta.

Don haka, hana tsangwama yana da muhimmanci irin na buƙatar inganta bincike da magance ta. Lokaci ya yi da za mu maido da aminci, da aiki tare, da kuma mutunci da ‘yancin ɗan-adam.

Shekarar 2026 za ta ita zama lokacin samun wannan babban sauyi.

A karon farko, duka ƙasashen nahiyar sun bayar da bayanai ga Hukumar Lafiya ta Duniya, wata alama da ke nuna ƙaƙƙarfar aniyarsu gabaɗaya.

Ƙasashe da dama sun kawo rahoton cewa ba a samu faruwar cuta a yara ba cikin shekaru masu yawa. Wasu kuma suna faɗaɗa tsarin gano cutar, da shigar da batun kuturta a harkar lafiyar fata. Wannan cigaba ya nuna za a iya kawar da cutar idan shirin ya ɗore.

Manufar ofishin WHO na Yankin Afirka a nahiyar da abokar haɗin-gwiwarta, shi ne tallafa wa wannan yunƙuri: ƙarfafa saka-ido, taimakon tawagogin da ke aiki a fili, tabbatar da samun magani ga kowa, da ɗaukaka yanayin ta yadda waɗanda abin ya shafa za su iya rayuwa ba tare da tsangwama ba. Kawar da cutar kuturta na nufin kare lafiya tare da kare mutunci.

Taron da za a yi a Brazzaville kan kawar da kuturta zai zama muhimmin mataki na Shirin Raba Afirka da Cutar Kuturta , inda za a nemi ministocin lafiya su ayyana babban mataki daidai da yanayin ƙasashensu.

A 2026, ba batun faɗar aniya ake ba, batu ne na cimma sakamako. Kuma akwai kayan aiki. Akwai bayanai. An tattaro ƙasashe da masu ba da tallafi. Yanzu ne lokacin kawo sauyi don samun cigaba.

Tuni Afirka ta nuna cewa za ta iya shawo kan babbar barazanar lafiyar jama’a, saboda kawar da tarin cutukan yankuna masu zafi da aka yi. Bari mu mayar da batun kawar da cutar kuturta ya zama labarin nasararmu ta nan gaba a yankinmu.

Marubuciyar, Dr. Dorothy Achu, ita ce Shugabar sashen Cutuka Masu Yaɗuwa da Na Yankuna Masu Zafi a Hukumar Lafiya ta Duniya, reshen Afirka.

Rumbun Labarai
Daga ƙasusuwa zuwa abin kwaɗayi: Orenge, abincin da ke sanya santi a Nairobi
Yadda A-Daidaita-Sahu na mata zalla ke sauya sufuri a jihar Kano ta Nijeriya
Kafafen sada zumunta na da alaƙa da raguwar farin ciki a faɗin Afirka da wasu yankuna - Rahoton 2026
Kuomboka: Ƙayatattun al'adun Masarautar Zambia mai shekara 300
Ƙalubalen sauyin yanayi a Afirka: Asarar rayuka, tafiyar ruwa da gidaje da rashin tabbas
An haifi wasu ‘yanbiyun gwaggwon biri da ke da wuyar samu karo na biyu a Congo DRC
Yadda raguwar kudin tallafi ke kai mutane kabari a Afirka
Yaya kaifin basira da fahimtar tausayi yake tsakanin giwaye?
Lailatul Qadri: Dare guda mai darajar watanni 1,000
Mohbad: Taƙaddama game da ko marigayi mawaƙin Nijeriya shi ne uban ɗansa na asali
Mata da 'yanmata na cikin mafi munin bala'i da ƙasƙanci a Gaza - MDD
Azumi da Ciwon Suga: Shawarwarin ƙwararrun Lafiya ga Musulmai a watan Ramadan
An gano ƙwarangwal ɗin wata babbar dabbar dinosaur mai kama da tsuntsu a Hamadar Nijar
Yadda Harsuna 2,000 suka sa Afirka ta zama nahiya mafi yalwar lugga a duniya
Ramadan a Gaza: Falasɗinawa na kokawa kan yadda yaƙi ya hana su abubuwan da suka saba lokacin azumi
Cibiyar Al’adu ta Yunus Emre ta haɗa Turkiyya da Nijeriya ta hanyar fasaha
Yadda azumin Ramadan ke inganta lafiyar jiki
Dalilan da za su ba lallai a fara azumin Ramadan na 2026 ranar Laraba ba a Nijeriya
Dalilin da ya sa harshenku na asali ke tsara duk wani yare da kuke magana da shi
Dalilin da ya sa har yanzu kuturta ke cikin cututtukan da ke addaba da barazana ga ɗan'adam