| Hausa
AFIRKA
1 minti karatu
Gabon ta dakatar da kafafen sada zumunta har sai baba-ta-gani
Hukumomi a Gabon sun ce an ɗauki matakin da shafukan sada zumunta ne sakamakon yadda ‘yan gwagwarmaya ke amfani da shafukan sada zumuntan don saɓa dokokin Gabon ta hanyar yaɗa “abubuwa marasa kyau na cin mutunci da ƙiyayya.”
Gabon ta dakatar da kafafen sada zumunta har sai baba-ta-gani
Gwamnati ta bayar da umurnin dakatarwa nan take "har sai baba-ta-gani." / Reuters

Gabon ta dakatar da wasu shafukan sada zumunta, inda ta bayyana cewa wasu saƙonnin da ake wallafawa ka iya zama barazana da hukumomi da tsaron ƙasar, kamar yadda hukumar da ke sa ido kan sadarwa ta ƙasar ta sanar a wata sanarwa.

Hukumar Sadarwa ta Gabon ta bayar da umarnin dakatarwar nan take "har sai baba-ta-gani," ba tare da fayyace waɗanne shafukan matakin ya ɗauka ba.

Kungiyar da ke sa ido kan intanet NetBlocks a ranar Laraba ta ce an dakatar da shafukan Meta da YouTube da TikTok a Gabon. sa

Hukumar Sadarwa ta Gabon ta ce ‘yan gwagwarmaya na amfani da shafukan sada zumuntan don saɓa dokokin Gabon ta hanyar yaɗa “abubuwa marasa kyau na cin mutunci da ƙiyayya.”

An zaɓi Shugaban Gabon, Brice Oligui Nguema, a Afrilun bara, bayan ya jagoranci juyin mulki a Agustan 2023 wanda ya kawo ƙarshen mulkin fiye da shekaru 50 na tsohon shugaban ƙasa Ali Bongo.

Rumbun Labarai
Ghana ta kwashe 'yan ƙasarta 300 daga Afirka ta kudu yayin da ake zanga-zanga kan baƙin haure
Mutane uku sun mutu bayan motar fasinja ta yi karo da giwa a gandun dajin Uganda
Shugaban Senegal Faye ya naɗa sabon firaminista da zai maye gurbin Sonko
Adadin mutanen da Ebola ta kashe a Jamuhuriyar Kongo ya wuce 200
Shugaban Senegal Faye ya sallami Firaministansa Ousmane Sonko
Kenya za ta rage farashin man dizel bayan zanga-zangar da aka yi kan tsadar makamashi
Gwamnatin Jamhuriyar Nijar za ta ƙayyade kuɗin gidajen haya
Sierra Leone ta amince ta karɓi kashin farko na waɗanda aka taso ƙeyarsu daga Amurka
'Makashin Al Fasher' ya koma fagen daga a yaƙin Sudan: Rahoto
Nijar da China sun cim ma yarjejeniyar mai bayan watanni ana takaddama
Adadin mutanen da suka mutu a Congo saboda kamuwa da Ebola ya kai 131
Kenya ta kama wata mata bisa zargin damfarar Ba’amurke dala 431,000 a yarjejeniyar cinikin zinare
Dole Afirka ta daina bin umarnin manyan ƙasashen duniya
WHO ta bayyana ɓarkewar Ebola a Jamhuriyar Kongo a matsayin 'matsalar lafiya ta gaggawa'
Mutum 80 sun rasu a sabuwar ɓarkewar Ebola a Jamhuriyar Congo
Sojojin Sudan sun ƙwace iko da wani muhimmin birni a kusa da iyakar Habasha bayan arangama da RSF
Yakin Sudan: Yara na daga gomman da aka kashe a arangamar makonni biyu a Kordofan
Nijar na son ƙara adadin jihohinta daga 8 zuwa 19 da kuma sauya sunayen wasu jihohim
Shirin 'Big Catch-Up': Kokarin da ya kawo alluran rigakafi miliyan 100 ga yaran Afirka da aka manta
Ghana za ta kwashe ɗaruruwan 'yan ƙasarta daga Afirka ta Kudu bayan hare-haren ƙin jinin baƙi