Kocin Kano Pillars, Babangaru Muhammad ya bayyanan abin da ya sa ƙungiyar ta samu ta lallasa ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Bendel Insurance ta Benin da ci huɗu da nema a wasan mako na 33 da suka yi a gasar Firimiyar Nijeriya ranar Lahadi a filin wasa na tunawa da mariagayi Sani Abacha da ke Kofar-Mata a Kano.
A wata hirar da ya yi da manema labarai bayan wasan Babangaru Muhammad, ya yaba wa ‘yanwasansa game da yadda suka aiwatar da shirin ƙungiyar yadda ya kamata.
Muhammad ya ƙara da cewa ƙungiyar ta yi nazari game da wasanta na baya inda ta kasa taɓuka wani abin a zo a gani, sannan suka yi gyare-gyare da ya kamata su yi.
“Mun zauna a matsayin ƙungiya kuma muka magance matsalolin da aka samu a wasanmu na baya.
“Na gode wa Allah cewa a yau mun yi nasara sosai.
“Samun ƙwallaye da yawa hakan yana da muhimmanci ga tsiranmu a wannan kakar,” kamar yadda ya bayyana.
Yadda suka zura ƙwallayen a raga
Karawar ta samu halartar ɗimbin mutane inda aka nishaɗantar da magoya bayan ƙungiyoyin da zura ƙwallaye a raga jim kaɗan bayan an fara wasan.
Mustafa Jibrin ne ya buɗe zura ƙwallo a raga minti 23 da fara karawar, kafin Chidozie Okorie ya ƙara zura ƙwallo ɗaya a raga bayan minti 10, lamarin da ya sa magoya bayan Masugida suka yi ta murna.
Bendel Insurance ta yi ƙoƙarin dawowa da ƙarfi yayin da Kano Pillars ta riƙe ƙwallo kuma take juya wasan yadda take so.
Masu masauƙin baƙin sun ci gaba kai samame bayan hutun rabin lokaci inda Muhammad Aminu da Bernard Ovoke suka ƙara zura ƙwallaye a raga a minti 81 da minti 85 da fara wasa lamarin da ya tabbatar da nasarar Pillars.
















