| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
Jami’an Kwastam na Nijeriya sun kai ziyarar aiki Nijar don ƙarin ilimi kan dabarun tsaro
Tsaron kan iyakoki da tattara bayanan sirri da haɗin kai da dakarun tsaro ne jigon tafiyarsu wadda ta bayyana matakai da za su iya ƙarfafa ikon aikin gwamnatocin ƙasashen biyu.
Jami’an Kwastam na Nijeriya sun kai ziyarar aiki Nijar don ƙarin ilimi kan dabarun tsaro
Jami'an kwastom na Nijeriya tare da na Nijar a taron da suka yi a Yamai / Actu Niger

A wani ɓangare na haɗin kai tsakanin hukumar kwastam ta Nijeriya da ta Nijar, jami’an kwastam goma sha uku na Nijeriya sun kai wata ziyara ta neman ƙarin ilimi a Yamai babban birnin Nijar daga ranar 14 zuwa 21 ta watan Nuwamba don nazari kan yadda takwarorinsu ke yaƙar barazana daga ƙetare.

Sa ido kan iyakoki da musayar bayanan sirri da haɗin kai da dakarun tsaro su ne muhimman jigogi na wannan ziyarar wadda ke da burin gano matakai da za su iya ƙarfafa ikon aiki na hukumomin biyu.

Tawagar ta jami’an kwastam na Nijeriya a ƙarƙashin jagorancin Mataimakiyar Kontrola IG Etim, ta ƙunshi jami’ai goma sha uku da ke da matsakaicin matsayi a hukumar Kwastam ta Nijeriya da suke cikin wasu ɗalibai da ke karatu a makarantar horas da jami’an kwastam da ke Gwagwalada, a Abujan Nijeirya.

Kafar watsa labarai ta Actu Niger ta ruwaito cewa ziyarar wani ɓangare ne na tsarin inganta ƙwarewar jami’an da kuma ba su damar samun ƙarin girma zuwa mataki na manyan jami’ai.

Tawagar ta samu tarbar mataimakin daraktan hukumar kwastam ta Nijar, Kanal Mohamed Siddo Yacouba.

Ganawar ta bai wa ɓangarorin biyu damar tattauna muradun gwamnatocinsu biyu da kuma ƙalubalen da suka shafi haɗin kai na kwastam tsakanin ƙasasehn biyu.

Bayan wannan tattaunawar ne jami’an Nijeriya suka kai ziyara Ma’aikatar Kuɗin Nijar inda suka samu tarbar babban sakataren ma’aikatar.

Ƙarfafa dangantaka

Tawagar ta Nijeriya ta samu tarba mai kyau daga wajen sakatare janar na Ma’aikatar Kuɗi ta Nijar.

Ya yi maraba da ‘yan tawagar kuma ya yaba wa tsarinsu, yana mai ba su ƙwarin gwiwa don a ci gaba da ƙarfafa haɗin kai tsakanin Nijar da Nijeriya.

Ya mayar da hankali kan muhimmancin kare da ƙarfafa dangantaka tsakanin ƙasashen biyu, musamman a fannin tsaron kan iyakoki.

Ya ce ya yi imanin cewa ci gaba da musayar bayanai da dangantaka ta aiki a wannan fannin na da muhimmancin bai wa ƙasashen biyu damar iya inganta haɗa ƙoƙarinsu da kuma tabbatar da tsaro a kan iyakokinsu tare.

Bayan wannan ganawar ne dai, aka fara aikin ziyarar ƙarin ilimin a ɗakin taron Ma’aikatar Kuɗi. Wannan mataki na farko na aikin ya buɗe wasu jerin tattaunawa da suka mayar da hankali kan yadda jami’an hukumar kwastam ta Nijar ke fama da barazana daga ƙasashen ƙetare.