A wani yunƙuri na faɗaɗa rassanta a Afirka, ranar Litinin Kamfanin Hannun Jari na Nijeriya, NGX, ya sanar da cewa ya sayi kashi 10% na jarin Kasuwar Hannun Jari ta Nairobi, a Kenya.
Wannan ciniki ya bai wa NGX damar fitowa a dama da ita a Gabashin Afirka, inda ake da kasuwannin hannun jari masu ƙarfi, don faɗaɗa hannun jarinta a wajen Nijeriya.
Sai dai NGX bai ambaci darajar kason da ya saya ba. Ko a 2024 ma, NGX ya zama mai hannun jari a Kasuwar Hannun Jari ta Habasha.
Kasywar ta Nairobi ta samu cigaba a muhimmancinta a gwamman shekarun baya-bayan nan, yayin da masu zuba jari ke amfani da hakan don hanzarta haɓaka tattalin arziƙin yankunansu, da samar da sabbin dabaru kamar kuɗin dijital na M-Pesa na kamfanin Safaricom.
Neman haɗewa
An shirya za a shigar da hannayen jari a Kasuwar Hannun Jari na Nairobi Securities Exchange Plc, a Jadawalin Kasuwannin da ke Kangaba ƙarƙashin MSCI.
Kasuwannin hannun jari a Afirka suna yunƙurin kusantar junansu, duk da cewa a baya-bayan nan an ga wasu ƙalubalen gudanarwa da na ginin tsari, yayin neman tara kuɗaɗen jari daga wata ƙasa zuwa wata.
Kamfanin NGX Group ya ce mallakar tana tallafa wa manyan muradun haɗewar yankunan, faɗaɗa dabarun zuba jari, da darajar masu hannun jari a dogon zango.
Shugaban NGX Group, Umaru Kwairanga ya faɗa a wata sanarwa cewa, "Kasuwannin hannun jari na Afirka suna kan ganiyar cigaba, lokacin da burin haɗewa ya tashi daga fata zuwa dabarar zahiri."
Ginshiƙin hada-hadar kuɗi a gabashin Afirka
Babban Jami’in Gudanarwa na kamfanin NGX, Temi Popoola, ya ce Kenya ita ce ginshiƙin hada-hadar kuɗi a gabashin Afirka, kuma zuba jari a kasuwar Nairobi zai faɗaɗa tushen samar da ribar jari daga wajen Nijeriya ga kamfanin NGX Group.
Popoola ya ƙara da cewa, "Tuni duka kasuwannin biyu suka nuna abin da tasirin haɗa-kai zai iya cimmawa ga kamfanoni masu jari, da masu hada-hadar hannayen jarin, da kuma tabbatuwar alaƙar masu mallakar hannun jari".





















