| Hausa
AFIRKA
4 minti karatu
Ghana na samun tan 62 na sinadarin mercury a kowace shekara ta hanyoyin da ba su dace ba
Ci-gaba da amfani da sinadirai masu guba a gundumomin da ake haƙar ma'adinai na barazana ga ruwa da muhalli da lafiyar jama'a, in ji su.
Ghana na samun tan 62 na sinadarin mercury a kowace shekara ta hanyoyin da ba su dace ba
Ƙananan masu haƙr ma'adinai na cikin waɗanda ake ganin suke amfani da sinadarin mai guba / Reuters (Wire)

Ghana na samun tsakanin tan 42.5 zuwa 62 na sinadarin mercury a kowace shekara ta hanyoyin da ba su dace ba inda ake amfani da su wajen haƙar ma’adinai na ɗaiɗaikun mutane da kuma haƙar zinare mai yawa, kamar yadda masu ruwa da tsaki a harkar suka bayyana.

Ci gaba da amfani da abubuwa masu guba a cikin gundumomin da ake haƙar ma’adinai na barazana ga ruwa da yanayi da lafiyar jama’a, in ji su.

Dr Sylvester Akpah, Shugaban kamfanin Smart Innovation Ghana Limited ne ya bayyana hakan a wani taron tattaunawa da ofishin jakadancin Amurka a Accra ya shirya a madadin ofishin da ke kula da Muhalli da Kimiyya da Fasaha da Lafiya a yankin Yammaci da Tsakiyar Afirka na Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka a ƙarƙashin shirin Ƙwararru kan Ruwa.

Ya ce sinadarin na mercury na shiga ƙasar ne ta hanyoyin da ba a tantance ba kuma ƙananan masu haƙar ma’adinai da ƙananan kamfanonin masu haƙar ma’adinai ne suke amfani da shi.

Dr Akpah ya ce fiye da mutum miliyan 2.5 ne suka dogara kai tsaye ko kuma a kaikace kan ƙananan kamfanoni na haƙar ma’adinai don samun abincinsu, lamarin da ya sa amfani da mercury ba bisa ƙa’ida ba ya zama wani abu na sanya babbar damuwa.

Ya ce gubar mercury ta fi shafar al’ummomin da ke haƙar ma’adinai a lardunan na Yammaci da Ashanti da Gabashi da kuma na Tsakiyar Ghana, inda wasu koguna suka guraɓace.

Dr Akpah ya bayyana Tarkwa da gundumomi maƙwabta a matsayin wuraren da ke ƙarƙashin matsi mai yawa na muhalli kuma ya ce ci-gaba da gurɓata abubuwa na barazana ga samun ruwan sha mai aminci.

Ya ce mercury na ci gaba da shiga ƙasar ta hanyoyin da ba su dace ba duk da matakan da aka saka a tashohsin jirage ruwan ƙasar.

Dr Akpah ya kuma bayyana rashin wata ma’aikata da ke kula da amfani da mercury da sauran matakai na sa ido a fannin haƙar ma’adinai a matsayin wani ƙalubale ga sa ido kamar yadda ya kamata.

Ya ce masu haƙar ma’adinai da mazauna kusa da wurin suna haɗuwa da sinadarin ta hanayar amfani da mercury yau da kullum wajen sarrafa zinare, wanda zai iya shafar ƙoda da huhu da ƙwaƙwalwa.

Dr Akpah ya yi kira da a ƙara matsi wajen aiwatar da dokokin da ke akwai da kuma amfani da wasu fasahoi wajen rage da kuma hana amfani da mercury gabaɗaya daga baya wajen haƙar ma’adinai na ƙananan kamfanoni.

Ya bayyana fasahohi na fitar da zinare a matsayin wani mataki da za a iya ɗaukawa a madadin sinadarin, amma ya ce amfani da su ya kasance abin da aka taƙaita duk da zuba jarin da ake yi wajen shigowa da kayayyaki.

Dr Akpah ya bayyana cewa Ghana ta rattaɓa hannu kan yarjejeniyar Minamata Kan Mercury, wata yarjejeniyar ta ƙasa da ƙasa da aka yi da zummar kare lafiyar bil-Adama daga gurɓata yanayi na mercury, amma ya ce kawo yanzu akwai matsala wajen ƙaddamar da ita.

Farfesa Daniel Nukpezah na ma’aikatar Sashin nazari kan Muhalli da Shara, a Jami’ar Ghana, ya ce gurɓata yanayi na mercury na buƙatar ƙarin sa ido mai ƙarfi da kuma tsare-tsare na gudanarwa.

Ya ce mercury wani ƙarfe ne mai guba da ba ya narkewa a cikin muhalli, amma yana tafiya ta iska da ruwa da ƙasa da cikin ƙasa da abubuwa masu rai.

Farfesa Nukpezah ya ce za a iya sauya mercury zuwa methylmercury a wani muhalli na cikin ruwa, inda zai taru cikin kifaye da ya kuma shiga cikin jerin abincin ɗan Adam.

Ya bayyana cewa ƙwayoyin halittu a cikin ƙasa suna sauya mercury da aka saka cikin ruwa zuwa methylmercury, wanda halittun cikin ruwa suka haɗiya.

Farfesa Nukpezah ya ce tarywar mercury na ƙaruwa ne yayin da kifaye da suka fi girma ke cin ƙananan halittu, lamarin da ke ƙara haɗuwar mutane da sinadarin ta hanyar abinci.

Ya ce haɗuwa da sinadarin na iya faruwa ta hanyar shaƙar gurɓataccen iska da sha da cin gurɓataccen ruwa da kifi, da haɗuwa da gurɓatccen ƙasa da kuma shiga cikin harkar haƙar ma’adinai.

Farfesa Nukpezah ya bayyana haƙar ma’adinai na ɗaiɗaikun mutane da na ƙananna masana’antu a matsayin wani muhimmin tushen gurɓace abubuwa na mercury a Ghana domin masu haƙar ma’dinai suna amfani da sinadarin a matsayin wani abun da ba shi da tsada sosai wajen fitar da zinare daga duwatsu.