| Hausa
TURKIYYA
5 minti karatu
Har yanzu Afirka na jiran a cika mata alƙawurran da aka ɗauka kan sauyin yanayi, in ji Gabon a COP31
“Saboda haka, muna matuƙar buƙatar wannan taron COP da kuma ciyar da ajandar amfani da tsarin gargaɗin farko gaba,” in ji shi.
Har yanzu Afirka na jiran a cika mata alƙawurran da aka ɗauka kan sauyin yanayi, in ji Gabon a COP31
Ministan Muhalli na Gabon Mouba Olouna da Daraktar UNE PInger Andersen a taron COP31./ Hoto: X@MoubaStephen

Fiye da shekaru goma bayan Yarjejeniyar Paris, har yanzu ƙasashen Afirka na jiran a cika alƙawurran da aka ɗauka domin ganin an samar da sakamako a zahiri, kamar yadda Ministan Muhalli da Yanayi na Gabon ya bayyana a taron COP31 da ake gudanarwa a Turkiyya.

“Afirka ta kwashe shekaru tana magana da kuma fafutukar ganin an aiwatar da Yarjejeniyar Paris, amma har yanzu ba mu ga an cim ma wani gagarumin sakamako a zahiri ba,” kamar yadda Stanislas Stephen Mouba Olouna ya bayyana.

Ya ce ƙara amfani da tsarin gargaɗin farko na ɗaya daga cikin muhimman abubuwa ukun da Gabon ta mayar da hankali a kansu a taron, tare da samar da ƙarin kuɗaɗen tallafi da suka dace da kuma inganta hanyoyin da za a bi wajen aiwatar da tsare-tsaren yaƙi da sauyin yanayi.

“Saboda haka, muna matuƙar buƙatar wannan taron COP da kuma ciyar da ajandar amfani da tsarin gargaɗin farko gaba,” in ji shi.

Afirka na fuskantar ƙaruwar zafi cikin sauri fiye da matsakaicin ƙaruwar zafin duniya, a cewar Hukumar Kula da Yanayi ta Duniya (WMO). Matsanancin yanayi da sauran abubuwan da ke da alaƙa da sauyin yanayi sun shafi aƙalla mutum miliyan 13 a faɗin nahiyar a shekarar 2025, inda ambaliyar ruwa ta kai fiye da rabin al'amuran da aka bayar da rahoton faruwarsu.

Ƙasashe 40 cikin 100 ne kawai a Afirka ke da cikakken tsarin gargaɗin farko da ya shafi haɗurra daban-daban.

A wani zama na COP31 da aka mayar da hankali kan tsarin gargaɗin farko a Afirka, Babbar Sakatariyar WMO, Celeste Saulo, ta bayyana Madagascar da Zimbabwe a matsayin misalan yadda hasashen yanayi zai taimaka wa gwamnatoci da hukumomi ɗaukar matakan kariya tun da wuri.

Ta ce hasashen yanayi na ba da damar ware kuɗaɗe da kuma ɗaukar matakan da suka dace kafin fari ya auku.

Shirin Muhalli na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNEP) ya yi hasashen cewa ƙasashe masu tasowa za su buƙaci dala biliyan 305 a kowace shekara nan da shekarar 2035 domin ɗaukar matakan daidaitawa da sauyin yanayi.

Sai dai waɗannan ƙasashe sun samu tsakanin dala biliyan 28.2 zuwa dala biliyan 31.7 ne kawai na tallafin ƙasashen duniya domin daidaitawa da sauyin yanayi a shekarar 2024.

Ko da an cim ma burin da aka sanya a COP30 na ninka wannan tallafi nan da shekarar 2035, UNEP na hasashen cewa kuɗaɗen za su kai ƙasa da kashi ɗaya bisa uku na jimillar buƙatun da aka yi hasashe.

‘Muna buƙatar magana da murya ɗaya’

Mouba Olouna ya yi kira ga ƙasashen Afirka da su ɗauki matsaya guda a Antalya, tare da neman shugabancin Turkiyya a COP31 ya taimaka wajen tabbatar da abubuwan da suka fi mayar da hankali a kansu.

“Muna buƙatar a ji muryar Afirka a sarari kuma a fayyace,” in ji shi. “Muna buƙatar magana da murya ɗaya.”

Ministan ya ce tattaunawar da ake yi a Antalya za ta zama tubalin gina taron COP32, wanda Habasha za ta karɓi baƙuncinsa a shekara mai zuwa.

“Za mu ci gaba da wannan tattaunawar a Habasha,” in ji shi, “amma muna buƙatar tabbatar da cewa dukkan abokan hulɗarmu suna sauraron abin da Afirka ta shafe gomman shekaru tana faɗa.”

Ya ce Gabon za ta goyi bayan ajandar shugabancin Turkiyya a taron, yana mai nuni da makamashi da kuma sarrafa shara a matsayin wasu daga cikin abubuwan da ƙasashen Afirka suka fi mayar da hankali a kansu.

Ya kuma ce Gabon na son faɗaɗa haɗin gwiwarta da Turkiyya zuwa ɓangaren kamun kifi da sauran fannoni, bisa kyakkyawar alaƙar da ke tsakanin ƙasashen da kuma jarin da Turkiyya ta zuba a fannin samar da ababen more rayuwa.

Gabon na neman kuɗaɗe domin kare dazuzzukanta

Mouba Olouna ya bayyana samar da kuɗaɗe a matsayin wani fanni da tallafin ƙasashen waje da ake samu a halin yanzu bai wadatar ba.

Ya ce dazuzzuka sun mamaye kashi 88 cikin 100 na ƙasar Gabon, kuma ƙasar na buƙatar ƙarin hanyoyin samar da kuɗaɗe masu inganci domin kiyaye su, bayan shekaru da dama ana fuskantar matsalolin sare bishiyoyi da lalata dazuzzuka.

Gabon ta samu tallafin farko na dala miliyan 17 a shekarar 2021, a ƙarƙashin wata yarjejeniyar dala miliyan 150 da Shirin Kare Dazuzzukan Afirka ta Tsakiya (CAFI), bayan ƙwararru masu zaman kansu sun tabbatar da raguwar hayaƙin da ke haddasa ɗumamar yanayi sakamakon sare bishiyoyi da lalata dazuzzuka.

A watan Agusta, Gabon ta ƙaddamar da wani sabon shirin haɗin gwiwa mai suna Gabon Infini, wanda ke da burin samar da kuɗaɗen da suka kai dala miliyan 200 cikin sama da shekaru 10.

Mouba Olouna ya ce Gabon na son ci gaba da amfani da tallafin kuɗi da kuma tsarin biyan kuɗaɗe bisa sakamakon da aka tabbatar, tare da jawo ƙarin jarin daga kasuwannin kuɗi.

“Muna buƙatar kasuwannin kuɗi su fahimci irin rawar da dazuzzukanmu ke takawa, domin hakan zai taimaka wajen samar da ƙarin kuɗaɗe,” in ji shi.

Ya ce shirin Gabon na yaƙi da sauyin yanayi na ƙasa na buƙatar zuba jari mai yawa a fannin samar da makamashi da rage hayaƙin da ke fitowa daga masana'antar mai, da kuma bunƙasa sabbin fannoni irin su yawon buɗe ido mai kiyaye muhalli.

Ya kuma yi kira da a ƙarfafa haɗin gwiwar da za ta iya “kawo sauyi a zahiri”, tare da taimaka wa ƙasashe wajen cika alƙawurran da suka ɗauka na rage hayaƙin da ke haddasa ɗumamar yanayi da kuma samar da kuɗaɗen da ake buƙata.