Wata babbar kotun tarayyar Nijeriya a babban birnin ƙasar Abuja ranar Talata ta yi wa mutum biyar da aka samu da laifin ta’addanci hukunce-hukunce ciki har da ɗaurin shekara 20.
Kazalika kotun ta tura wani mutum da ake zargi da ta’addanci a gidan waƙafi bayan ya musanta zargin.
Hakan na faruwa ne yayin da gwamnatin tarayyar ƙasar ta shiga sabon mataki na shari’a ta bai-ɗaya wa mutum 500 da ake zargi da aikata ta’addanci.
Mai Shari’a M. O. Olajuwon ta sa a jiye Babagana Umar a hannun hukumar tsaro ta farin kaya ta DSS bayan ya musanta tuhuma uku da ke da alaƙa da tallafa wa Boko Haram.
An tuhumi Umar da “ba da tallafi da gangan ta hanyar samar da kayan gyara ga Boko Haram,” tare da samar da itacen hura wuta ga ƙungiyar ‘yanta’addan a adajin Sambisa a shekarar 2022.
An kuma tuhume shi da samun “bayanai game da wuri da kuma yadda Boko Haram take aika-aikarta, waɗanda da za su sa a kai ga kama tare da gurfanar da mutanen nan… amma bai bayar da su ga ko wace hukumar tsaro ba.”
Kotun ta ɗaga shari’ar Umar zuwa zamanta na gaba.

A wata shari’ar ta daban a kotun kuma, Mai Shari’a Olajuwon ta yi wa Yusuf Tuggar Abacha ɗaurin shekara 20 bayan ya amsa laifin kasancewa ɗan ƙungiyar Boko Haram, da ƙin ba da bayanai game da wani ɗan ƙungiyar da kuma kasancewa cikin masu kai hare-hare na ƙungiyar.
Kazalika, a wata shari’a mai kama da wannan a gaban Mai Shari’a Binta Nyako, an samu wasu mutum huɗu da laifi kuma aka yi musu hukunci daban daban.
Wani da ya amsa laifin kasancewa ɗan ƙungiyar Boko Haram, da kuma ba ta tallafi na kaya da sarrafa kuɗi da ke da alaƙa da ƙungiyar, an yi masa ɗaurin shekara 10 kan ko wace tuhuma, inda dukkan ɗaurin za su tafi a lokaci ɗaya.
“Ina yi wa wanda aka samu da laifin ɗaurin shekara 10 kan ko wace tuhuma daga ranar da aka kama shi kuma ɗaurin za su tafi tare… Kuma zai yi zaman gyaran hali tare da cire masa tsattsauran ra’ayi,” in ji Mai Shari’a Nyako.
An yi wa Isa Ali ɗaurin shekara 10 sakamakon bai wa Boko Haram tallafin jigila, kuma aka yi watsi da tuhuma ta kasancewa ɗan ƙungiyar, bayan ya musanta zargin.
Kazalika, Auwal Bello zai sha ɗaurin shekara 10 sakamakon taimaka wajen samar wa masu aikata ta’addanci kuɗi, ciki har da canza kimanin N750,000 da kuma biyan N20,000 ga ƙungiyar.
An yi wa Shehu Bukar ɗaurin shekara 20 sakamakon samar wa Boko Haram shanu da awaki.
Mai Sharia’a Nyako ta bayyana laifinsa a matsayin “mai muni sosai” kuma ta yi watsi da neman sassaucin masu kare shi.
“Ina masa ɗaurin shekara 20 daga ranar da aka kama shi. Za a kuma gyara mishi hali da kuma warware masa tsattsauran ra’ayinsa,” in ji ta.
Dukkan waɗanda aka samu da laifin an ba da umarnin a gyara musu hali tare da warware tsattsauran ra’ayinsu, inda ma’aikatar tsaron cikin gida za ta zaɓi gidajen yarin da za a tura su domin zaman kaso.
Sabuwar shari’a ta bai-ɗaya da gwamnatin tarayya take yi a matakinta na tara alƙalai 10 ne ke gudanar da ita inda suke zama a lokacin hutun Easter domin gaggauta shari’ar.
Antoni Janar kuma Ministan Shari’a na Nijeriya, Lateef Fagbemi (SAN), ya tabbatar da cewa duk da cewa waɗanda ake zargi 500 ne ake son a yi wa shari’a, guda 227 aka kai gaban kotu a ranar farko ta shari’ar.









