| Hausa
WASANNI
3 minti karatu
Kungiyoyin Gasar Firimiya ta Ingila sun yi asarar dala biliyan 1 na kudin-shiga: Rahoto
Kashe kuɗaɗe don sayo 'yanwasa ya yi yawan da ba a taɓa gani ba, wanda ya janyo masoya ƙwallo suna fushi kan kuɗin da ke fita waje yayin da ake neman su biya kuɗin tikita da tsada.
Kungiyoyin Gasar Firimiya ta Ingila sun yi asarar dala biliyan 1 na kudin-shiga: Rahoto
Kungiyoyin Premier League sun tafka gagarumar asara duk da cewa sun samu kudaden shiga da suka kai matakin tarihi na fam biliyan 6.8 ($9.2 biliyan). / AP

A duniya ana yi wa Gasar Firimiya kallon tauraruwa wajen samar da kuɗaɗen shiga, amma gamammen rahoto kan hada-hadar kuɗi na ƙungiyoyin gasar ya nuna cewa a kakar da ta gabata ƙungiyoyin sun tafka asarar dala biliyan 1 a garin neman nasara a filin wasa.

Duk da tara kuɗaɗen shiga na fam biliyan 6.8 a kakar 2024/25 a matsayin jimillar kuɗaɗen shiga, kuɗaɗen da suka fita sun ci gaba da wuce kuɗaɗen shigowa, saboda hauhawar farashi a kasuwar cinikin 'yanwasa, da albashin 'yanwasa, da kuɗaɗen dillalai.

Chelsea ta kafa wani rakod marar daɗi na tafka asarar kafin haraji mafi girma a tarihin Gasar Firimiya na fam miliyan 262 a shekarar kuɗi da ta ƙare ran 30 ga Yunin 2025.

Salon Chelsea na kwaso haziƙan matasa daga sassa daban-daban na duniya ba tare da tsoro ba ya zama mummunan abin misali, amma su ɗin wani ɓangare ne na matsalar da ta shafi tarin ƙungiyoyi.

Tottenham, wadda ke zullumin faɗowa daga gasar Firimiya, baya ge cewa ita ce ta tara mafi arziƙi a duniya, ta samu asarar fam miliyan 121 a kakar da ta gabata, duk da ƙaruwar kuɗaɗen shiga daga sabon filin wasanta mai ninkin -amfani, ga kuma kofin Europa da ta lashe.

Kuɗaɗen cinikayyar 'yanwasa

"Matsalar Gasar Firimiya ita ce ana sanya ƙungiyoyi su kashe kuɗi fiye da iyaka," in ji masani kan harkokin kuɗi a ƙwallon ƙafa, Kieran Maguire ga AFP.

"A ƙarshe abian ya koma takarar tara makamai wajen gogayya kan ɗauko 'yanwasa ta hanyar biyan kuɗin sauya kulob da na albashi."

Alƙaluman kakar 2024/25 ba su ma ƙunshi cikakken adadin fam biliyan 3 da ƙungiyoyin Gasar Firimiya suka kashe kan kuɗin canja 'yan wasa a kasuwar bazarar bara ba, wanda ya karya tarihin da ya gabata da fam miliyan 650.

Sayo Alexander Isak da Liverpool ta yi kan fam miliyan 125 ya kafa sabon rakod na ƙungiyar ƙwallo a Ingila, kuma wani ɓangare ne na kashe kuɗin da Liverpool ta yi a kasuwar bazarar da ya kai fam miliyan 450, wanda har yanzu bai haifar da sakamako mai ganuwa ba.

Kuɗaɗen albashin na ci gaba da ƙaruwa, har sun kai fam biliyan 4.4 a kakar da ta gabata, wato ƙarin kashi tara cikin ɗari kan shekarar da ta gabace ta, wanda ya haura ƙarin kashi bakwai cikin ɗari da aka samu a kuɗaɗen shiga.

'Ana iya ɗaukar' asarorin

Kudin da ake kashewa kan dillalai shi ma ya kai sabuwar ƙololuwa, abin da ya ƙara ɓata ran magoya ƙwallo, ganin yadda kuɗaɗe ke fita daga wasan, yayin da ake ƙara musu farashin tikiti.

Za a gabatar da sabbin ƙa'idojin kashe kuɗi a kakar wasa mai zuwa, waɗanda za su mai da hankali kan iyakance jimillar kuɗin tawaga guda, don ya yi daidai da kuɗaɗen shiga.

Kashe kuɗaɗen kan albashi, kuɗin canja 'yan wasa da dillalai bai kamata ya wuce kashi 85 cikin 100 na kuɗaɗen shiga ba, tare da saka mafi tsaurin iyaka ta kashi 70 cikin 100 ga ƙungiyoyin da ke fafatawa a gasar UEFA.

Sai dai kuma, waɗannan canje-canjen ba za su yi tasiri sosai wajen rage asara ba, saboda an cire kuɗaɗen gudanarwa da suka tashi zuwa fam biliyan 1.9, ga ƙungiyoyin Gasar Firimiya a kakar da ta gabata.