| Hausa
DUNIYA
4 minti karatu
Turkiyya da kasashe 7 sun yaba wa Birtaniya kan hana kawo kaya daga haramtattun mazaunan Isra'ilawa
Ministocin harkokin waje sun yi kira ga al'ummar duniya da su ɗauki ƙwararan matakai kan abubuwan da suke tallafawa da kuma wanzar da haramtattun matsugunnen Isra'ilawa.
Turkiyya da kasashe 7 sun yaba wa Birtaniya kan hana kawo kaya daga haramtattun mazaunan Isra'ilawa
'Yan share-wuri na Isra'ila da ba bisa ka'ida ba sun taru a gaban gidajen Falasdinawa a kauyen Qusra a ranar 12 ga watan Agusta, 2026. / Hoto: AFP

Ministocin harkokin waje na Turkiyya, Masar, Indonesia, Jordan, Pakistan, Qatar, Saudi Arabia da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa sun yi maraba da matakin da gwamnatin Birtaniya ta ɗauka na hana shigo da kayayyaki daga matsugunan haramtacciyar ƙasar Isra'ila a yankin Falasdinawa da aka mamaye da kuma taƙaita ayyukan da ke da alaƙa da irin waɗannan matsugunan.

A cikin wata sanarwa ta haɗin gwiwa da suka fitar a ranar Laraba, ministocin sun bayyana fatan cewa wannan mataki zai taimaka wajen jan hankalin al'ummar duniya su ɗauki irin wannan mataki bisa ga dokokin ƙasa da ƙasa da kuma hukunta kungiyoyi da ɗaiɗaikun mutane da suke da hannu a ayyukan haramtattun matsugannai.

Sun kuma yi maraba da sanarwar haɗin gwiwa kan mafita ta samar da ƙasashe biyu da ministocin harkokin waje na Canada, Denmark, Finland, Faransa, Iceland, Ireland, Norway, Poland, Portugal, Sifaniya, Sweden da Birtaniya suka fitar.

Ƙasashe 12 sun tabbatar da aniyarsu ta gabatar da takunkumi da kuma goyon bayan takunkumin Turai kan cinikayyar kayayyaki daga haramtattun matsugunai a ƙarƙashin dokokin ƙasa da ƙasa, ko kuma su yi la'akari da waɗannan da sauran matakai bisa ga ƙa'idojin ƙasa da ƙasa.

Minisitojin ƙasashen takwas sun buƙaci al'ummarrin duniya da su ɗora a kan waɗannan matakai tare da ɗaukar matakai na zahiri don kawo ƙarshen ayyukan da ke tallafawa ko kuma ci gaba da matsayar da ƙasar haramtacciyar Isra'ila a yankin Falasdinawa da aka mamaye.

Sun ce matakan da aka sanar sun yi daidai da dokokin kasa da kasa da kuma ƙudurorin Majalisar Dinkin Duniya masu alaƙa da su, ciki har da ƙudurin Kwamitin Tsaro ta Majalisar Dinkin Duniya mai lamba 2334 da kuma shawarar da Kotun Duniya ta bayar a ranar 19 ga Yuli, 2024.

Haramtacciyar mamayar Isra'ila

Sanarwar ta ambato wajibci kan dukkan ƙasashe na ƙin amincewa da yanayin da ya taso daga mamayar haramtacciyar ƙasar Isra'ila a yankin Falasɗinu a matsayin doka, kuma kada su bayar da tallafi ko taimako wajen wanzar da yanayin da mamayar ta haifar.

Ministocin sun sake nanata kiransu ga Isra'ila da ta soke dukkan matakan da aka ɗauka dangane da ayyukan matsugunan, da kuma wasu matakai da nufin sauya yanayin yanki da yanayin al'ummar yankin Falasdinu da aka mamaye.

Sun kuma jaddada cewa Gaza muhimmin bangare ne na yankin Falasɗinu da aka mamaye, kuma sun yi kira da a yi "cikakken aiwatar" da shirin shugaban Amurka Donald Trump na kawo ƙarshen yaƙin kisan ƙare dangi na Isra'ila a Gaza.

Ministocin sun ce ya kamata a aiwatar da shirin don tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali, da magance matsalar jin’ƙai, da sauƙaƙe sake ginawa da farfaɗo da yankin, da kuma shimfiɗa harsashin zaman lafiya mai ɗorewa.

Sun sake jaddada cewa "hanya ɗaya tilo da za ta iya cim ma zaman lafiya mai adalci, ɗorewa kuma cikakkiya ita ce aiwatar da mafita ta samar da ƙasashe biyu ta hanyar kafa ƙasar Falasɗinu mai zaman kanta, mai 'yancin kai, mai haɗin kai, mai ɗorewa bisa ga iyakokin 4 ga Yuni, 1967, tare da Gabashin Ƙudus a matsayin babban birninta.

Ministocin harkokin wajena na ƙasashe 12 sun sanar a cikin wata sanarwa ta haɗin gwiwa a ranar Talata cewa za su sanya ko kuma su yi la'akari da takunkumin ciniki kan kayayyaki daga haramtattun matsugunan Isra'ilawa a Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye.

Ƙasashen sun ce ayyukan Isra'ila a Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye suna lalata damar samun mafita ta ƙasashe biyu kuma sun jaddada buƙatar kiyaye yiwuwar kafa ƙasar Falasɗinawa.

Nan da nan Isra'ila ta sanar da cewa za ta rufe ofishin jakadancin Burtaniya a Gabashin Ƙudus da aka mamaye, wanda ke yi wa Falasɗinawa hidima, a matsayin martani ga matakan.