| Hausa
DUNIYA
3 minti karatu
Trump ya sa hannu kan sabuwar dokar takunkumi ga Rasha: China da India na iya fuskantar sabon haraji
Dokar da Trump ya amince da ita a ranar Jumma’a ta shafi ɓangarorin makamashi da tsaro na Rasha, da kuma Shugaba Vladimir Putin da wasu manyan jami’an gwamnati.
Trump ya sa hannu kan sabuwar dokar takunkumi ga Rasha: China da India na iya fuskantar sabon haraji
Modi na Indiya na musabaha da shugabannin Rasha da Sin yayin taron kolin BRICS karo na 18 a New Delhi.

Shugaban Amurka Donald Trump ya sanya hannu kan wata doka da ta ba da izinin ƙaƙaba sabbin takunkumai da nufin matsa wa Rasha lamba kan yaƙin da take yi a Ukraine, jim kaɗan bayan Majalisar Dokokin Amurka ta amince da dokar a wannan makon.

Dokar da Trump ya amince da ita a ranar Jumma’a ta shafi ɓangarorin makamashi da tsaro na Rasha, da kuma Shugaba Vladimir Putin da wasu manyan jami’an gwamnati. Haka kuma, dokar ta shafi hamshaƙan attajiran Rasha, ’yan uwansu, wasu mutane daga ƙasashen waje, da bankunan Rasha da cibiyoyin kuɗi.

Ta kuma shafi abin da ake kira da jerin jiragen ruwa na ɓoye na Moscow, wato jiragen dakon mai da ake amfani da su wajen kauce wa takunkumin ƙasashen Yamma. Dokar ta kuma bai wa Trump ikon ƙaƙaba harajin da ya kai kashi 100 cikin 100 kan manyan masu sayen man fetur da iskar gas daga Rasha, ciki har da China da India.

Majalisar Wakilan Amurka da Jam’iyyar Republican ke jagoranta ta amince da ƙunshin dokokin da ƙuri’a 262 kan 159 a ranar Laraba.

Dokar za ta kuma shafi kamfanoni da wasu ɓangarorin ƙasashen waje da ke tallafa wa sojojin Rasha, tare da faɗaɗa takunkumin da ya shafi Iran.

Sai dai faɗaɗa ikon Trump na ƙaƙaba haraji ya haifar da rarrabuwar kawuna da ba kasafai ake gani ba tsakanin ’yan Democrat, waɗanda galibi ke goyon bayan Ukraine, amma suka yi tir da bai wa Trump ƙarin iko kan harkokin kasuwanci da haraji.

Zelenskyy Ya Yi Godiya ga Amurka

Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelenskyy, ya bayyana a baya cewa amincewa da dokar na da muhimmiyar ma’ana, tare da gode wa ’yan majalisar dokokin Amurka.

“Abin da ya fi dacewa wajen girmama tunawa da Lindsey shi ne a aiwatar da tanade-tanaden wannan doka gaba ɗaya kuma cikin gaggawa,” in ji Zelenskyy a ranar Jumma’a, yana magana ne kan marigayi Sanata Lindsey Graham, wanda ya jagoranci yunƙurin ganin an amince da dokar.

A ranar Alhamis, Indiya ta ce za ta ci gaba da sayen mai daga Rasha “ta hanyoyi daban-daban na samo makamashi.”

Sa hannu da Trump ya yi kan dokar ya kuma zo ne mako guda kafin ganawarsa da Shugaban China, Xi Jinping, a Washington.

Dokar ta bukaci Trump ya kakaba harajin da ya kai kashi 100 cikin 100 cikin kwanaki 30 kan duk kayayyakin da ake shigowa da su Amurka daga ƙasashen da suka fi shigo da ɗanyen mai ko iskar gas daga Rasha, da kuma duk wata ƙasa da ta ci gaba da sayen mai ko iskar gas daga Rasha cikin sanin cewa hakan ya saba wa dokar, kwanaki 30 bayan dokar ta fara aiki. Haka kuma, za a iya ƙaƙaba harajin kan ƙasashen da ke cikin manyan ƙasashe biyar da ke taimaka wa Rasha wajen kauce wa takunkumi.

Sai dai lamarin bai shafi ƙasashen da ke shigo da ƙasa da kashi 15 cikin 100 na iskar gas ɗin da Rasha ke fitarwa, kuma suka ɗauki manyan matakai wajen rage dogaro da wannan iskar gas.

China da Indiya na daga cikin manyan ƙasashe masu sayen man Rasha. Sai dai masu sukar dokar sun ce ta bai wa jami’an Amurka damar zaɓar ƙasashe da dama da Amurkar za ta iya matsa wa lamba, saboda dokar ba ta ambaci wata ƙasa kai tsaye ba, kuma ba ta fayyace yadda za a ƙididdige jerin ƙasashe biyar da ake magana a kai ba.

Rumbun Labarai
Trump ya ce rashin ba shi kyautar Nobel ta Zaman Lafiya 'abin kunya ne'
Faransa ta ce za ta bai wa Saudiyya kariya a ɓangaren man fetur ɗinta
HRW: Tasa ƙeyar ’yan Ci-rani zuwa Afirka da Amurka ke yi azabtarwa ce
Trump na shirin kai wa Iran hari kafin zaɓen tsakiyar wa'adi a Amurka - rahoto
WHO ta yi kira ga Rasha da ta yi gaskiya game da rahotannin mutuwa sakamakon annobar ciwon huhu
Amurka ta janye dukka jiragen yaƙinta na B-1 daga sansanin sojin saman Birtaniya saboda tsoron hari
Trump ya yi gargaɗin cewa yaƙi da Iran zai zo ƙarshe ko ta halin ƙaƙa 'nan ba da jimawa ba’
An ceto baƙin-haure 260 a gaɓar tekun Mauritania
Sau takwas sojojin Amurka na yunƙurin kashe kansu a cikin USS Abraham Lincoln, in ji gwamnatin Trump
Kwamitin Zaman Lafiya na Duniya zai gabatar da shirin farfado da Gaza na dala biliyan $2.45: Rahoto
Erdogan a UNGA: Gaza ce sansanin tsare mutane mafi muni da rashin tausayi da abin kunya a zamaninmu
Trump ya yi wa Iran barazana, ya kira ICC ‘marar gaskiya‘, ya sauya sunan AI zuwa ‘SI’
Amurka ta kai 'yan ci-rani fiye da 25,000 da ta kora zuwa ƙasashen da ba su da alaƙa da su: Bincike
Antonio Guterres ya nemi a bai wa Afirka kujerun dindindin a Kwamitin Tsaro na MDD
Kasashen Yamma na shirin yaƙi da Rasha: Lavrov
Ƙanwar Kim Jong-un ta ce 'wawaye' ne kawai ke tunanin Koriya ta Arewa za ta miƙa makaman nukiliyarta
Taliban na neman ƙulla dangantaka da Amurka da sharaɗin a duba illolin yaƙin Afghanistan
Wuta za ku je idan ba ku jefa ƙuri'a a zaɓen 'yan majalisa ba, in ji Trump ga 'yan Republican
Shekaru 25 bayan 9/11, Amurkawa na tsoron ta’addancin cikin gida fiye da barazanar hari daga waje
Turkiyya da kasashe 7 sun yaba wa Birtaniya kan hana kawo kaya daga haramtattun mazaunan Isra'ilawa