| Hausa
DUNIYA
2 minti karatu
Amurka ta kai 'yan ci-rani fiye da 25,000 da ta kora zuwa ƙasashen da ba su da alaƙa da su: Bincike
Gwamnatin Trump ta cim ma yarjejeniyoyi da ƙasashe 35 inda ta ware aƙalla dala miliyan 410 don tallafa wa aikin korar.
Amurka ta kai 'yan ci-rani fiye da 25,000 da ta kora zuwa ƙasashen da ba su da alaƙa da su: Bincike
Mutanen da aka kora daga Amurka, ciki har da 'yan kasar Mexico, sun hallara a cikin wata cibiyar tantancewa a filin jirgin saman La Aurora da ke birnin Guatemala, 21 ga Agusta, 2026. / AP Archive

Amurka ta kori fiye da mutane 25,000 zuwa ƙasashen da ba su da wata alaƙa da su, ƙarƙashin yarjejeniyoyin da gwamnatin Trump ta cimma, a cewar wani bincike.

Aƙalla mutane 25,447 ne aka aika zuwa ƙasashe 28 ya zuwa ranar 31 ga Agusta, a cewar binciken da Forbidden Stories, wata ƙungiyar labarai mai zaman kanta da ke Paris, ta gudanar. Gwamnatin Amurka ba ta bayyana waɗannan alƙaluman ba a hukumance.

Tun bayan da Shugaba Donald Trump ya hau mulki a watan Janairun 2025, gwamnatinsa ta cim ma yarjejeniyoyi da ƙasashe 35 domin karɓar baƙin-haure da aka kora zuwa ƙasashen da ba ƙasashensu na asali ba. Cikakkun bayanan yarjejeniyoyin ba a bayyana su sosai ba.

Binciken, wanda haɗakar ‘yan jarida 72 daga kafafen yaɗa labarai 26 a ƙasashe 15 suka gudanar, ya ƙunshi tattaunawa da fiye da mutane 100 da aka kora, jami’an gwamnati, lauyoyi da masana.

Ƙoƙarin cim ma yarjejeniyoyi

Takardun cikin gida na Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka da jaridar The Washington Post, ɗaya daga cikin mambobin ƙungiyar da ta gudanar da binciken, ta samu, sun nuna cewa Amurka ta shirya kashe aƙalla dala miliyan 410 a wani yunƙuri na cim ma yarjejeniyoyi da ƙasashe da za a aika baƙin-hauren.

Daga cikin wannan kuɗi, an ware dala miliyan 81 ga gwamnatocin da suka rattaba hannu kan yarjejeniyoyin, yayin da aka ware fiye da dala miliyan 178 ga Ƙungiyar Kula da ‘Yan ci-rani ta Duniya (IOM), sannan aka ware fiye da dala miliyan 123 ga Hukumar Kula da ’Yan gudun Hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya.

Galibi dai Ofishin Fitar da ‘Yan ci-rani na Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ne ke tattaunawa kan waɗannan yarjejeniyoyi. An kafa wannan sashe ne a shekarar 2025 a matsayin wani ɓangare na sake fasalin ma’aikatar.

Fadar White House, yayin da take mayar da martani kan binciken, ta ce baƙin-hauren da ake aikawa ƙasashe mutane ne waɗanda ƙasashensu na asali suka ƙi karɓarsu, ciki har da waɗanda aka bayar da umarnin kora daga ƙasar kuma suka nemi kada a mayar da su ƙasashensu na asali.

A ranar 18 ga Satumba, wata kotun ɗaukaka ƙara ta tarayya ta Amurka ta bayar da umarnin dakatar da korar mutane zuwa ƙasashen, tana mai cewa ba a bai wa baƙin-hauren sanarwa a kan lokaci ko damar ƙalubalantar korar tasu ba.