Hukumar tsaron gaɓar tekun Mauritania ta bayyana cewa ta ceto baƙin-haure 260 a cikin wasu kwale-kwale guda biyu, ciki har da yara 17 a gaɓar tekun Atlantik na ƙasar a ranar Lahadi.
Hukumar ta ce baƙin-hauren suna cikin kwale-kwale biyu ne da suka taso daga Banjul na ƙasar Gambia, kuma sun shiga yanayin firgici bayan abincinsu ya ƙare tare sannan sun yi ɓatan-hanya bayan man kwale-kwale ya ƙare.
An hango su ne a yankin gaɓar tekun babban birnin Nouakchott na ƙasar Mauritania bayan sun shafe kusan kwana bakwai a cikin teku, in ji hukumar.
Sanarwar hukumar ta ce, cikin waɗanda aka ceto akwai 'yan ƙasar Senegal 132 da 'yan Gambia 120, da 'yan Guinea huɗu, da kuma wasu da dama daga ƙasashen Yammacin Afirka.
Baya ga yara 17, an kuma samu mata 61 da ke cikin kwale-kwalen, a cewar sanarwar.
Tsawon shekaru, dubban mutane musamman matasa suna yunƙurin bi ta wannan hanya mai hatsari ta Tekun Atlantik a cikin kwale-kwale ruwa waɗanda suke cika maƙil da mutane, kana galibinsu ba sa cikin yanayi mai kyau, domin isa Turai ta hanyar tsibiran Canary na ƙasar Sifaniya.
Mutane da yawa kan tsere wa talauci su bi wannan hanya mai cike da hatsari, sakamakon yadda ƙasashen Turai suka tsaurara matakan bayar da biza da kuma sanya tsauraran dokoki a kan iyakokinsu.


















