Amurka ta janye dukka jiragen yaƙinta na B-1 masu dabarun kai hari daga sansanin sojin saman Birtaniya mako guda bayan da aka kama mutane da dama a sansanin bisa zargin shirya ayyukan ta'addanci, in ji wani jami'in Pentagon.
An ajiye jiragen yaƙin B-1 guda goma sha biyu a sansanin sojin saman RAF Fairford, wanda ke arewa maso yammacin London. Amurka ta yi amfani da jiragen wajen kai hare-hare a Iran.
“Duk da cewa matakan tsaron aiki sun hana mu tabbatar da tsaron kayan aiki da sojojinmu a daidai lokacin da abin ke faruwa, yanzu za mu iya tabbatar da cewa dukkan jiragen saman Amurka masu kai hare-haren bama-bamai, waɗanda aka jibge a sansanin RAF Fairford, an mayar da su sansanoninsu da ke Amurka,” a cewar wani mai magana da yawun Pentagon a ranar Lahadi.
Birtaniya tana da "hujjoji masu ƙarfi" da ke nuna cewa Iran tana da hannu a wani shirin hari da ake zargin za a kai sansanin, kamar yadda Firaministan Birtaniya Andy Burnham ya bayyana.
Tehran ta ce zarge-zargen ba su da tushe kana ta kira jakadan Birtaniya a Tehran kan batun.
Jaridar Wall Street Journal ce ta fara fitar da rahoton cewa an ɗauke jiragen daga sansanin saboda fargabar yiwuwar kai hari a wurin.
"Hannun wani ɗan ƙasar waje"
Gwamnatin Birtaniya ta bai wa Amurka damar amfani da jiragenta da ke Fairford don kai hare-hare a Iran.
Tashar jiragen sama ta Gloucestershire ta kasance babbar cibiyar kai hare-haren bama-bamai a lokacin yaƙin Iran.
Rahotannin sun bayyana cewa wasu mutane biyar sun yi balaguro zuwa Fairford a cikin fararen motocin a-kori-kura uku a ranar Lahadin da ta wuce.
‘Yansandan Birtaniya sun ce ba a samu wani abu mai fashewa a cikin motocin ba, ko da yake suna ɗauke da man fetur mai yawa.
'Yansanda sun kama mutanen bayan ɗaya daga cikinsu ya tuntuɓe su don sanar da su game da zargin ta’addancin.
An kama mutum na shida, mai ruwa-biyu, ɗan ƙasar Birtaniya da Iran, bayan wasu kwanaki bisa zargin hannu a shirin ta'addancin.
Daga baya aka sake shi bisa beli.
Shugaban Amurka Donald Trump ya ce waɗanda ke da hannu a cikin wannan makircin sun shirya yin "babbar ɓarna", yayin da Sakataren Harkokin Wajen Amurka Marco Rubio shi ma ya nuna da cewa da "hannun wani ɗan ƙasar waje cikin zargin."


















