Jamus ta fuskanci mutuwar mutane 15,800 sakamakon tsananin zafi a wannan bazarar yayin da Turai ta fuskanci jerin mummunan zafi, in ji Cibiyar Robert Koch (RKI) a ranar Alhamis.
Mutane masu sama da shekaru 75 ne suka fi fama da wannan matsala, inda aka samu mutuwar mutane kusan 9,600 saboda zafi a cikin mako guda a ƙarshen watan Yuni lokacin da yanayin zafi ya wuce daraja 40°C, in ji Cibiyar Lafiyar Jama'a ta Ƙasa.
An samu mutuwar mutane 4,000 saboda tsananin yanayin zafin a tsakanin ƙarshen watan Yuli da tsakiyar watan Agusta, a cewar RKI.
Cibiyar ta ce adadi mafi yawa na waɗanda suka mutu a baya saboda tsanantar zafi shi ne mutuwar mutane 8,900 a shekarar 2018. Wani bincike na likitoci ya ƙiyasta mutuwar mutane 10,000 saboda tsanantar zafin a shekarar 1994.
Zafi da fari sun shafi yawancin Turai a wannan bazarar, wanda hakan ya zama sanadin ƙara yawan mace-mace da suka shafi zafi yayin da suke haifar da wutar daji, suna lalata amfanin gona da kuma rage yawan ruwa a manyan koguna.
Zafi mai tsanani na iya haifar da mutuwa kai-tsaye ta hanyar yanayi kamar bugun zuciya, amma galibi yana kashe mutane idan ya hadu da cututtukan zuciya, huhu ko ƙoda.
Hukumar RKI ta tattara bayanan mace-mace da ke da alaƙa da tsananin zafi a cikin shekaru goma da suka gabata, tana mai amfani da alƙaluman mace-mace a cikin makonnin lokacin bazara tana kwatanta na lokacin da ake fuskantar tsananin zafi da wanda ba a fuskantar tsananin zafin.



















