Ma’aikatan filin jiragen sama na Frankfurt na Jamus biyu sun mutu sakamakon cizon sauro da ake tunanin cewa sun shiga ƙasar ne ta jirgin sama, kamar yadda hukumomin tsaron birnin suka bayyana a ranar Laraba.
Jami’an filin jiragen saman sun bayyana daga farko cewa ɗaya daga cikin ma’aikatan ya rasu inda ma’aikata shida suka kamu da cutar zazzaɓin cizon sauro.
Hukumar Robert Koch Institute (RKI) mai hana yaɗuwar cututtuka a Jamus ta ce tana ganin wani nau’in sauro da aka shigo da shi ƙasar ta jirgin sama ne ya haddasa cutar.
Ana kan yi wa sauran waɗanda suka kamu da cutar magani a asibiti, in ji wani mai magana da yawun filin jiragen saman.
Hukumar RKI ta Jamus ta ce shekarar 2023 ne lokaci na ƙarshe da aka samu ɓullar cutar a wani filin jirgin saman ƙasar. Rashin yawan samun cutar na nufin zai iya ɗaukar lokaci kafin a gano cewa mutum ya kamu da cutar, lamarin da zai ƙara yawan raɗaɗin ciwon.
Ana kan yi wa sauran ma’aikatan magani, kamar yadda mai magana da yawun filin jiragen saman ya bayyana, yana mai ƙarawa da cewa an kafa tarkunan sauro a filin jiragen saman.
Cibiyar nazarin cututtukan yanki mai bazara a birnin Antwerp, na ƙasar Belgium, ta ce za ta yi bincike kan ƙwayoyin cutar malaria da ke cikin jinin mara lafiyar.
Cutar zazzaɓin wadda ke yaɗuwa ta ƙwayoyin cutar da sauro ke yaɗawa na da alamu da suka haɗa da jin tashin zuciya da ciwon kai da zazzaɓi mai tsanani da jin sanyi.
Cutar na haddasa ɗaruruwan dubban mace-mace a ko wace shekara, yawanci a Afirka Kudu da Sahara.
Cutar na da magani kuma marasa lafiya da suka gano cutar da wuri na warkewa gabaɗaya daga cutar.
















