Zanga-zanga ta ɓarke a wurare da dama a India kan ƙyamar dokar ɗan ƙasa da aka zarge ta da nuna wariya ga Musulmai bayan gwamnatin Firaiminista Nerandra Modi ta aiwatar da dokar, kwana daya kafin a bayyana ranar da za a gudanar da babban zaɓe.
A ranar Litinin zanga-zanga ta ɓarke a jihar Assam ta gabashi da jihar Tamil Nadu a kudanci da yamma, bayan an sanar da fara aiki da dokar, kamar yadda hukumomi suka bayyana ranar Talata.
Babu wani rahoto na ta'adi ko arangama da jami'an tsaro.
A ranar Litini, jam'iyyar ƴan kishin ƙasa ta Hindu Bharatiya Party (BJP) ta Narandra Modi ta sauya dokoki don aiwatar da sauyi kan dokar Zama Ɗokar Zama Ɗan Ƙasa (CAA) don sauƙaƙa wa ƴan gudun hijira waɗanda ba Musulmai ba daga ƙasashe uku na kudancin Asia masu Musulmai da yawa damar samun shaidar zama ɗan ƙasa.
Fara amfani da dokar a 2019 ta haifar da gagarumar zanga-zanga da rikicin ƙabilanci, inda aka kashe mutane da dama, abin da ya tilastawa gwamnati jinkirta fara aiwatar da ita.
A Chennai, babban birnin Tamil Nadu, masu zanga-zangar sun kunna kyandir ranar Litinin sannan suka ringa taken ƙyamar dokar.
A Assam, masu zanga-zangar sun ƙona kwafin dokar, sannan suka ringa rera take a ranar Litinin da daddare, sannan jam'iyyun hamayya na yankin sun yi kira da a gudanar da yajin aiki ranar Lahadi.
Mutane da dama sun yi adawa da dokar a Assam saboda suna tsoron za ta ƙara yawan masu neman mafaka daga Bengaladesh da ke maƙwabtaka.