Juma'a 16 ga Agustan 2024
1435 GMT — Za a ci gaba da tattaunawar tsagaita wuta a Gaza a mako mai zuwa a birnin Alkahira
Manyan jami'ai daga Masar da Qatar da Amurka za su sake ganawa a birnin Alkahira kafin karshen mako mai zuwa, da fatan cimma yarjejeniyar kawo karshen mummunan yakin da Isra'ila ke yi a Gaza, in ji sanarwar hadin gwiwa.
Sanarwar ta ce tattaunawar ta kasance da gaske, mai ma'ana, kuma an gudanar da ita cikin yanayi mai kyau.
Masu shiga tsakani sun dage cewa abin da aka tattauna ya yi daidai da ‘ka’idojin da shugaban Amurka Biden ya gindaya a ranar 31 ga watan Mayu da ya bukaci janye sojojin Isra’ila daga Gaza domin a sako mutanen da aka yi garkuwa da su.
Masu shiga tsakani za su yi aiki a cikin kwanaki masu zuwa kan cikakken bayani game da shawarar tsagaita wuta a Gaza, a cewar sanarwar, da fatan cimma yarjejeniya bisa sharuddan da aka yanke ranar Juma'a.
Sai dai wani jami'in Hamas ya ce bayanan da aka raba wa 'ƙungiyar game da sakamakon tattaunawar tsagaita wuta ba su yi daidai da abin da aka amince da shi a shawarwarin Biden ba.
0845 GMT — Qatar ta ce tattaunawar tsagaita wuta a Gaza ta kai wani muhimmin mataki
Firaministan Qatar kuma Ministan Harkokin Wajen ƙasar Mohammed bin Abdulrahman Al Thani ya ce tattaunawar shiga tsakani don aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wuta a Zirin Gaza ta cimma mataki mai muhimmanci a tattaunawar da ya yi da takwaransa na riƙon ƙwarya na Iran Ali Bagheri Kani, wanda ya jaddada buƙatar matsa wa Isra'ila ta dakatar da "kisan kare dangi" a kan Falasdinawa.
"A cikin wata tattaunawa ta wayar tarho da firaministan Qatar kuma ministan harkokin wajen kasar, Mohammed bin Abdulrahman Al Thani, mun tattauna kan sabbin laifukan gwamnatin Isra'ila a Gaza da kuma hanyoyin dakatar da su," in ji Kani a wata sanarwa bayan tattaunawar a ranar Juma'a.
Kani ya ce sun tattauna kan sulhun da ake yi a Doha da nufin cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza da kuma yarjejeniyar yin garkuwa da su tsakanin Isra'ila da Hamas.
"Al Thani yana ishara ne da taron da Qatar ta shirya game da shawarwarin tsagaita wuta, yana mai bayyana sakamakon wannan mataki na tattaunawar a matsayin mai muhimmanci," in ji jami'in na Iran.
Sauran labarai👇
0842 GMT — Malaysia ta ceto Falasɗinawa 127 daga Gaza
Malaysia ta yi nasarar kwashe Falasdinawa 127 daga Gaza, lamarin da ya kai su ga samun mafaka a kudu maso gabashin Asiya.
Mutanen sun haɗa da maza da mata da ƙananan yara, kuma sun isa sansanin sojin sama na Subang a cikin wani jirgin sama na Royal Malaysian Air Force.
Firaministan Malaysia Anwar Ibrahim ne ya ƙaddamar da wannan aikin ceto, wanda ya sanar da yin aikin a lokacin wani gangamin hadin kai ga Falasdinu a Kuala Lumpur a ranar 4 ga watan Agusta.
0742 GMT — Sojojin Isra'ila sun ba da umarnin sake kwashe mutane a Gaza
Sojojin Isra'ila sun ba da sabbin umarni na ficewa ga mazauna yankuna da dama na tsakiya da kuma kudancin Gaza wadanda sojojin suka ayyana a matsayin "yankin da ke da aminci".
A cikin wata sanarwa da ta fitar, sojojin Isra'ila sun umarci mazauna yankunan arewacin Khan Younis da ke kudancin Gaza da kuma yankunan gabashin Deir al-Balah da ke tsakiyar Gaza da su ƙaurace wa yankunan.
0405 GMT — Hamas ta yi Allah wadai da harin da Isra'ila ta kai a yammacin Gaɓar Kogin Jordan
Kungiyar Hamas ta yi Allah wadai da harin da wasu ‘yan Isra’ila suka kai ba bisa ka’ida kan ƙauyen Jit da ke gabar Yammacin Kogin Jordan da suka mamaye, inda suka kashe wani Bafalasdine tare da ƙona gidaje da motoci na wasu mazauna yankin.
A cikin wata sanarwa da ta fitar, ƙungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta yi kira da a yi tada ƙayar baya da kuma arangama da 'yan kama wuri zaunan.
Ta ƙara da cewa "Muna jimamin jarumtar shahidi Rashid Mahmoud Sada, wanda wasu tsagera suka kashe a kauyen Jit, kuma muna tabbatar da cewa wannan jinin tsaftataccen jinin ba zai tafi a banza ba, kuma ya zama tsinuwa ga mamayar."