Yevgeny Prigozhin ya jagoranci wani bore da bai yi nasara ba kan gwamnatin Rasha wata biyu da suka wuce. / Hoto: Reuters

Shugaban kamfanin sojojin haya na Wagner, Yevgeny Prigozhin, ya mutu a wani hatsarin jirgi a Rasha, a cewar Hukumar Kula da Sufurin Jirage ta kasar.

A ranar Laraba ne wani karamin jirgi ya yi hatsari a yankin Tver na birnin Moscow inda duk mutum 10 da suke ciki suka rasa rayukansu, in ji hukumar agajin gaggawa ta Rasha.

Kazalika wani shafin Telegram mai alaka da Kamfanin Wagner ya tabbatar da mutuwar Prigozhin a sanarwar da ya wallafa a shafin. Ya zargi gwamnatinn Rasha da alhakin kisan.

Shugaban Wagner Yevgeny Prigozhin na cikin jerin fasinjojin da ke cikin jirgin, a cewar rahotannin kafafen yada labaran Rasha.

Kazalika wani babban kwamandan Wagner Dmitry Utkin yana cikin jirgin.

"Wani karamin jirgi da ya tashi da birnin Moscow zuwa Saint Petersburg ya yi hatsari a kusa da kauyen Kuzhenkino a yankin Tver.

“Akwai mutum 10 a cikinsa jirgin da suka hada da ma’aikatansa uku. Bayanan farko-farko sun ce dukkan mutanen da ke cikin jirgin sun mutu,” a cewar Ma’aikatar Ayyukan Gaggawa ta kasar a sanarwar da ta saka a shafinta na Telegram.

Bore ga rudunar sojin Rasha

Prigozhin, mai shekara 62, ya jagoranci yin bore ga manyan dakarun sojin Rasha a tsakanin 23 da 24 ga watan Yuni, wanda Shugaba Vladimir Putin ya ce abu ne da zai iya jefa Rasha yakin basasa.

An kawo karshen boren bayan yarjejenya da kuma shawo kan Prigozhin da fadar Cremlin ta yi kan ya koma Belarus mai makotaka da Rasha. Amma an gan shi na kai komo a cikin Rasha duk da wannan yarjejeniya da aka kulla.

Prigozhin, wanda ya so kawar da Ministan Tsaro Sergei Shoigu da Valery Gerasimov, shugaban rundunar soji, a ranar Litinin ya yada wani faifan bidiyo da ke nuna yana wata kasa a Afirka.

AA